--
Sau 3 ina yiwa diyata cikin shege, sannan na kai ta asibiti a zubar mata da cikin a matsayin budurwata – Fasto

Sau 3 ina yiwa diyata cikin shege, sannan na kai ta asibiti a zubar mata da cikin a matsayin budurwata – Fasto




Wani fasto mai suna Oluwafemi Oyebola, mai shekaru 44, da ‘yan sanda suka kama a jihar Ogun, ya bayyanawa Daud Olatunji yadda ya dinga kwanciya da diyarshi har sai da yayi mata ciki sau uku.

Shin da gaske ne kana kwanciya da diyarka?

“Ubangijina ya hana kuji abubuwan shaidanci. Matata ta farko sunanta Deborah. Tana da ‘ya’ya uku, amma ta rasu a ranar 7 ga watan Oktobar 2016, sakamakon rashin lafiya. An binneta a cikin gidanmu dake Ijoko cikin jihar Ogun. Kafin mutuwarta, An bani mukami mai girma a coci. Bayan bani wannan mukami a Ajilete, an bani gidan da zauna nida iyalina.

“Shekara daya bayan mutuwar matata, watan Nuwambar shekarar 2017, na kira ‘ya’yana guda ukun, na sanar da su cewa ina so nayi aure. Sun ki amincewa dani, inda suka ce baza su yadda su zauna da ita gida daya ba. Haka suka rokeni akan nayi hakuri har zuwa lokacin da zasu kammala karatun su. A karshe dai duka mun amince akan ba zan sake aure ba. Diyata ta kammala difloma dinta. Ta biyun kuma an bata gurbin karatu na difloma ita ma, inda ita kuma karamar take aji biyu a sakandare.

Shekarar diyarka nawa wacce kayi mata cikin shege?

“Shekarunta 24, ta biyun kuma shekarunta 21, sai ta karshen kuma shekarun 18. Duka sun san da wannan lamari.

Daga ya ya wannan abu ya faru?

“Lamarin ya samo asali a watan Disambar shekarar 2017 da kuma Janairun 2018. Ta bayyana mini cewa ba tayi al’ada ba na wannan watan, bayan nayi jima’i da ita na farko. Hakan ya sanya na tsorata sosai sai na dauketa zuwa asibiti a Idi-Iroko don a zubar da cikin. Na biya N1,000. Na gabatar da ita a wajen malamar asibitin a matsayin budurwata. A watan Yunin shekarar 2018, na biyu ya sake faruwa, na sake kai ta wajen wannan malamar asibitin don ta zubar da cikin, a lokacin sai ta bani wani abu na tsarin iyali. Mako daya bayan zubar da wannan cikin na biyu, sai ta fara yi mini karar cewa cikinta yana ciwo.

Mai ka yi a lokacin?

“Na kai ta wajen sayar da magani na kauyenmu. Aka bata magani, sai ta warke daga ciwon cikin. Mako biyu bayan ta warke, sai aka kira ta bautar kasa (NYSC). Ta tafi aikin bautar kasar ta dawo a ranar 29 ga watan Disambar 2018. Sai ta sake tafiya Fatakwal a watan Janairun 2019. Na sha sanar mata a waya cewa ina da wacce nake so, kuma bata taba nuna bacin ranta ba,

na sanar da ita cewa zan auri matar kamar yadda addini ya tsara, kuma auren ba zai shafi ‘ya’yana ba. Bayan ta kammala bautar kasar ta dawo, sai ta rokeni akan za ta tafi fatakwal ta zauna a can sai naki yarda, na ce mata dole ta zauna da kannanta. Duk lokacin dana ji magana ta jima’i tsakanin uba da ‘ya, sai hankalina ya tashi, kuma na yiwa kaina alkawarin bazan sake bari haka ta faru tsakanina da ita ba.

Hakan ya sanya na matsa sai na auro wata matar. Muna da daki daban-daban, inda da ‘ya’ya mata guda biyu da kuma namiji daya. Matan guda biyu suna kwana a daki daya, yayin da shi kuma namijin yake kwana dakin shi daban. Jima’i da nake yi da ita ba wai ina yi saboda son raina bane saboda ita ba matata ba ce. Na kan ji hankalina ya tashi a duk lokacin da nake jima’i da ita, amma ban san ita yadda take ji ba.


Daga ya ya asirinku ya tonu?

“Abinda ya sanya asirin ya tonu shine, saboda na hana ta komawa Fatakwal. A wajen karshen watan Maris, 2020, sai ta zo ta sake samu na akan cewa za ta tafi Fatakwal. Sai nace mata ba za ta tafi ba, sai ta fara yi mini ihu. Sai naji haushi na mare ta, nake ce mata ni mahaifinta ne kuma Bible bai yadda da rashin biyayya ga iyaye ba. Mintuna kalilan bayan wannan sai ta dawo ta bani hakuri, na yafe mata, ban san cewa tana da wata a kasa ba. Ta taba gaya mini cewa za ta kunyata ni ta bata mini suna idan na mare ta.

“A ranar 1 ga watan Afrilu, 2020, sai ta dauki wayarta da takardunta ta gudu; ba mu san inda ta tafi ba. A ranar 14 ga watan Afrilu, sai ta kira ni a waya, ta ce kada ma na fara wahalar neman, saboda za ta zauna a inda take ta nemi aiki. A rana ta biyu, sai ta sake kirana, ta ce mini za ta sanya ni nayi dana sanin dukanta da nayi. Na bata hakuri amma taki yarda. Na sanar da duka ‘yan uwana akan su bata hakuri amma taki yarda.

Menene ta ce da har kace ita ce ta kawo kanta ka dinga jima’i da ita?

“Mako biyu bayan tara su da nayi, sai na kirata nake tambayarta shin da gaske suke yi ita da kanwarta akan cewa baza su bari nayi aure ba. Amsar da ta bani ita ce eh. Sai nake tambayarta daga yaya zanyi da kuma bukatar jima’i da nake da ita, sai tayi shiru na dan lokaci ta ce ba damuwa ita za ta dauki nauyin jima’i dani.

Cikin sauri na bukaci ta rufe bakinta, sai taki yadda. Ban canja komai ba daga cikin abinda na fada tun lokacin da aka kama ni a Owode. Abinda ya faru ya riga ya faru. Yafi na fadi gaskiya ko Allah zai ceto ni kuma ya yafe mini da nayi karya. Tun a wannan ranar ta ce za ta dinga kwanciya dani, kuma babu wanda zai taba jin sirrin mu. A wannan lokacin tana makaranta ne ma. Ban taba tunanin cewa shaidan ne yake yaudara ta ba. Lamarin ya faru tsakanin shekarar 2017 zuwa 2018.”


SOURCE:PRESSLIVES.COM

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Sau 3 ina yiwa diyata cikin shege, sannan na kai ta asibiti a zubar mata da cikin a matsayin budurwata – Fasto"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?