Sarauta: Sarkin Kano Aminu Ado ya hana yin Hawan kilisa a Kano
Tuesday, 14 July 2020
Comment
Sarkin Kano; Aminu Ado Bayero |
Majalisar masarautar Kano ta sanar da haramcin hawa dawakai da sunan kilisa a cikin babban birnin Dabo, tana mai gargadin cewa za a hukunta duk wanda ya sabawa wannan umarni.
Hakan yana kunshe cikin sanarwar da sakataren fadar kuma Turakin Kano, Alhaji Lamido Abdullahi Sanusi ya fitar yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin cikin tsohon birnin.
Lamido wanda shi ne shugaban kwamitin Durbar na masarautar Kano, a yanzu an haramta duk wani hawa na dawakai da sunan kilisa ko kuma hawan angwanci.
A cewarsa, irin wannan haye-hayen dawakai da sunan kilisa ko kuma hawan Durbar yana janyo mummunar barazana ta samun raunuka, asarar rayuka da dukiyar masu wucewa a kan hanyoyi.
Ya ce irin wannan sukuwa da ake yi a lunguna ko kan titunu tana haddasa barna da kuma muzgunawa al'ummar gari.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, masarautar Kano ta dauki wannan hukunci ne na dakatar da duk wani hawan dawakai biyo bayan korafe-korafen da ake gabatar mata na yadda lamarin ke janyo barazana a tsakanin al'umma.
Masarautar ta bayyana cewa, sukuwa, hawan Durbar, kilisa ko kuma hawan angwanci da ake gudanarwa a cikin birnin Kano ya kan haddasa rauni ga kananan yara da dattawa tare da janyo wasu miyagun ababe.
Gabanin ta bijiro da sabbin tsare-tsare, masarautar ta bayyana damuwa kan yadda ake hawan dawakai barkatai, da sukwane-sukwane marasa dalili a cikin lunguna da manyan hanyoyi.
A yayin jan kunne da gargadin cewa za a hukunta duk wanda aka kama ya saba wa doka, masarautar ta ce daga yanzu an dakatar da kilisar dawakai da aka saba yi bisa al'ada matukar ta haura dawakai 3 zuwa biyar.
Kamar yadda Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito, sanarwar ta bayyana cewa dole ne kuma masu hawan dawakan su kasance cikin kyakkyawar shiga da kamala, kuma ba a yarda a yi sukuwa a wuraren da ba su kamata ba.
SOURCE: LEGIT.NG
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Sarauta: Sarkin Kano Aminu Ado ya hana yin Hawan kilisa a Kano"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?