--
Rouhani: Akwai Hasashen Mutane Kimani Miliyon 25 Sun Kamu Da Cutar Korona A Iran

Rouhani: Akwai Hasashen Mutane Kimani Miliyon 25 Sun Kamu Da Cutar Korona A Iran


Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa akwai yiyuwan mutane kimai miliyon 25 sun kamu da cutar korona a kasar a cikin watanni 5 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a taron kwamitin yaki da cutar Korona a kasar a safiyar yau Asabar.

Shugaban ya kara da cewa ya zuwa yancu cutar korona ta kashe mutane dubu 14 a kasar sannan adadin wadanda suka kwanta a asbiti ya kai 200,000 sai dai nan gaba hasashen ya nuna cewa adadin zai ninka.

Shugaban Rouhani ya ce kasar Iran tana da magunguna cutar korona har guda biyar, sannan a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa za ta fara amfani da wani sabo.

Daga karshe shugaban ya kammala da cewa akwai hasashen mutane miliyon 30-35 zasu kamu da cutar nan gaba.

Yawan mutanen da suka kamu da cutar a cikin yan makonnin da suka gabata a nan birnin Tehran ya kara yawa, wanda hakan ya tilastawa gwamnatin kasar sake rufe wasu wuraren harkokin kasuwanci a wannan kano, wadanda ba’a dade da budesu ba.


Source: http://hausatv.com/

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Rouhani: Akwai Hasashen Mutane Kimani Miliyon 25 Sun Kamu Da Cutar Korona A Iran"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?