Rahoton siya wa da gidan N300m: Malami ya yi barazanar maka wata jarida a kotu
Monday, 13 July 2020
Comment
Rahoton siya wa da gidan N300m: Malami ya yi barazanar maka wata jarida a kotu. Hoto daga The Punch Source: UGC |
Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, ya bai wa mawallafan Sahara Reporters kwanaki 7 tak da su janye wallafarsu mai cike da 'bacin suna' da suka yi mishi ko kuma ya maka su a kotu.
Wannan na zuwa ne bayan rahoton da suka wallafa a yanar gizo inda suke ikirarin ministan ya bai wa babban dan sa Abdulaziz, kyautar gidan N300 miliyan a Abuja a matsayin kyautar aurensa. A wata takarda da Malami ya fitar ta hannun kakakinsa, Umar Gwandu, ya kwatanta rahoton da bacin suna, ya ce hakan ya bata masa suna a matsayinsa na minista kuma hakan ya matukar tada masa hankali.
Kamar yadda takardar tace, SaharaReporters ta wallafa abubuwa masu tarin yawa da za su iya bata masa suna. Ya ce kuma duniya za ta iya daukan hakan da gaske ba tare da wani bincike ba. Ya ce, a ranakun 10, 11 da 12 ga watan Yulin 2020, a abinda yayi kama da shiryayyen hari, sun yi wallafa masu cike da cin zarafi gareshi.
A don haka yayi kira garesu da su fito su bada hakuri a shafin farko na jaridu uku na kwanaki uku a jere ko kuma su fuskanci shari'a.
Ministan ya ce: "Akwai takaici idan aka gano cewa wallafar babu gaskiya, kagaggiya ce kuma bacin suna ce. "Tun daga ranar 10 ga watan Yulin 2020 lokacin da wallafar farko ta fita, na fara samun kira ta waya daga 'yan Najeriya, abokai, masu fatan alheri da abokan aikina a duk fadin duniya.
Da yawa sun nuna damuwarsu a kan wallafar. "Wannan miyagun wallafar an yi su ne domin zubar min da mutunci a idon mutane nagari. Wannan ya ci karo da dokokin Penal Code, kuma take hakkina ne wanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bani." Kamar yadda takardar ta bayyana, an yi wa wani babban lauya bayani a kan lamarin kuma rashin janye wallafar tare da bada hakuri a cikin lokacin zai sa su fuskanci shari'a.
SOURCE: legit.ng
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Rahoton siya wa da gidan N300m: Malami ya yi barazanar maka wata jarida a kotu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?