
Na fi karfin inyi fada da Dogara, ya yi kadan - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed
Wednesday, 29 July 2020
Comment
Gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed, ya siffanta tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da ya sauya sheka zuwa All Progressives Congress APC a matsayin annoba a siyasa. Ya zargi Dogara da kara kudi a kwangila a ayyukan da yakeyi a mazabarsa. Ya bayyana hakan ne yayinda daruruwan masoya daga kananan hukumomin Dass, Tafawa Balewa da Bogoro, da Yakubu Dogara ke wakilta suka kai masa ziyara gidan gwamnati ranar Talata.
Mun kawo muku rahoton cewa, Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya musanta dukkan zargin rashawa da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya kwatanta shi da su. Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin da ya karba bakuncin 'yan majalisa masu wakiltar mazabar Dass/Tafawa Balewa/Bagoro a Bauchi.
Dogara na wakiltar mazabar ne a majalisar wakilai. Tsohon kakakin majalisar wakilan ya zargi Gwamna Bala Mohammed da waskar da bashin N4.5 biliyan da ya karbo, kara kudin kwangila da watanda da kudaden karamar hukuma a matsayin dalilan da yasa ya bar PDP tare da komawa APC.
SOURCE: LEGIT.NG
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Na fi karfin inyi fada da Dogara, ya yi kadan - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?