--
Na bawa mijina dama yaje ya kwanta da duk macen da yake so babu damuwa – Mawakiya

Na bawa mijina dama yaje ya kwanta da duk macen da yake so babu damuwa – Mawakiya




Mawakiya ‘yar Najeriya, Seyi Shay ta bayyana cewa ba ta da damuwa ko kadan dan mijinta yana kwanciya da karuwai, duk da dai ta ce ita dai baza ta taba cin amanarsa ba.

Mawakiyar ta bayyana haka ne a lokacin wata hira da tayi tare da Seun Kuti a gidan rediyon Cool FM.

A lokacin hirar, taurarin sunyi magana akan shin auren namiji guda daya yana yiwuwa a wannan lokacin.

Seyi Shay a nata bangaren ta ce ita dai tayi alkawarin baza ta taba cin amanar mijinta na aure ba, sai dai ta cigaba da cewa babu damuwa ko kadan dan mijinta yana mu’amula da karuwai a titi.

Ta ce: “Mutane suna yin kuskure na ganin cewa maza ne kawai aka kyale su ci amanar aure. Mata suna ganin da sunyi aure, shikenan babu su babu wata rayuwa, maza za su iya yin duk wani abu da suke so, idan har baza su kama su ba.

“Na san mata da yawa za su zage ni akan abinda zan fada, amma zancen gaskiya ni bani da matsala don mijina yana mu’amala da wata a titi.

“Idan har suna da yawa to bani da matsala. Saboda idan guda daya ce, akwai yiwuwar zai iya fara sonta, amma idan suna da yawa na san cewa ni daya ce ta gaban goshin.”

Ga dai abinda ta ce a bidiyo:
                              
SOURCE: PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Na bawa mijina dama yaje ya kwanta da duk macen da yake so babu damuwa – Mawakiya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?