--
Musulmai sun bukaci a kama fitaccen Malami Ashraf Jalali, bayan ya zagi Nana Fadima diyar Manzon Allah

Musulmai sun bukaci a kama fitaccen Malami Ashraf Jalali, bayan ya zagi Nana Fadima diyar Manzon Allah




A wani bidiyo da yayi Dr Ashraf Jalali, ya ci mutuncin Fatima Zahra (RA), wacce take diya ce a wajen fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW), wannan magana da yayi dai ta kawo kace-nace matuka, inda mutane a kowanne yanki na duniya suka dinga kira da a kama shi.

Bidiyon da yayi da yaren Urdu, an fassara abinda ya ce da yaren Turanci, inda ya ce:

“Ita Fatima Zahra (RA) da take bata da laifi, hakan bai sanya ta zama tana da gaskiya ba, ba ta da gaskiya, kuma lokacin da ta nemi hakkinta, nan ma bata da gaskiya.”

Bayan wannan bidiyo ya yadu a kafafen sadarwa, mutane daga kasar Pakistan, Indiya, dama sauran Musulmi na duniya baki daya sun hau shafukansu na sadarwa suka dinga kira da a kama shi akan ya zagi Nana Fadima, wacce take diya a wajen Annabi Muhammad (SAW).

A matsayinka na Musulmi, tilas ne ka nuna soyayya ga Annabi Muhammad (SAW), da iyalan gidansa. Ga dai wasu daga cikin rubutun da mutane suka dinga wallafawa akan wanna magana ta shi:




Yayin da mutane ke kiran shi da munafuki, majalisar kasar Pakistan ita ma ta fara zanga-zanga a kanshi, inda dan majalisar kasar Imran Ali Shah, ya fito fili ya ce zai bawa Ashraf Jalali hukunci mai muni.




A nuna goyon bayanta akan maganar Imran Ali Shah, ‘yar majalisa Shagufta Jumani, ita ma ta bayyanawa majalisa cewa tilas ne a hukunta Ashfar, inda ta ce zamu sadaukar da kanmu da ‘ya’yanmu akan Fatima Zahra (RA).



A yadda wasu rahotanni suke nuni, an hana shi shiga birnin Kashmir baki daya.





A cewar ministan shari’ah na kasar Pakistan, Raja Basharat, ya sanar da majalisar kasar cewa tuni an shigar da karar shi kuma za a kamo shi nan bada dadewa ba.

Haka dan majalisa Kazim Peerzada, shi ma ya ce wannan magana da Ashraf Jalali yayi akan Fatima Zahra (RA), babban laifi ne na ta’addanci.


SOURCE: PRESSLIVES.COM


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Musulmai sun bukaci a kama fitaccen Malami Ashraf Jalali, bayan ya zagi Nana Fadima diyar Manzon Allah"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?