Mu mata bala’i ne da tashin hankali, ni kai na ina tsoron kai na – Jarumar fim
Tuesday, 14 July 2020
Comment
Fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya na Nollywood, Regina Chukwu tayi tambaya akan mai yasa mata mugaye ne. Ta yi wannan magana ne a lokacin da take sharhi akan dalilin da ya sanya wasu matan suke cin zarafin masu yi musu aiki.
Jarumar ta ce tayi mamaki, inda take ganin mata da ake tunanin suna da hakuri da kyakkyawar zuciya, ashe abin ba haka yake ba.
Ta ce: “Mata ina so nayi muku wata tambaya, dan Allah mai yasa mu mugaye ne? na kasa ganewa gaskiya, shin ba mune ya kamata mu zama masu tausayi ba? Daga yaya muka zama mugaye azzalumai, mai yasa muke yin haka, shin daga yaya ma zamu fara bayanin abubuwan zalunci da mata suke yi.
“Mai yasa muke mayar da masu yi mana aiki tamkar bayi? bai kamata nace bayi ba ma, mai yasa muka mayar da su tamkar dabbobi? Hatta dabbobi ba ayi musu cin zarafin da ake yiwa wasu yaran, mai yasa? Daga yaya zaki buga kusa akan mutum, daga yaya zaki yi amfani da dutsin guga mai zafi a jikin mutum, daga yaya zaki dauki barkono ki sanya a gaban yarinya,
daga yaya zaki sanya yarinyar mutane a cikin bandaki ta dinga kwana, mai yasa, dukan mu mata ne, kada mu yi watsi da wannan zuciyar ta tausayi da Allah ya bamu. Idan yaron ko yarinyar basu jin magana ku mayar da su wajen iyayensu, ba dole bane.”
SOURCE: PRESSLIVES.COM
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Mu mata bala’i ne da tashin hankali, ni kai na ina tsoron kai na – Jarumar fim"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?