
Matar da ta kware wajen saye da sayar da jarirai ta shiga hannu yayin da take cinikin wani sabon jariri
Saturday, 4 July 2020
Comment
An kama wasu mata guda biyar a lokacin da suke cinikin sayar da wani sabon jariri da aka haifa mako biyu da suka wuce.
An kama Mrs Roseline Nwokocha daga Umuahia tare da ‘yar uwarta, Chioma, a Fatakwal, jihar Rivers. Chioma dai ta raka ta ne don ta ga jaririn, kamar yadda Roseline ta sanar da ‘yan sanda.
Wannan dai ba shine karo na farko ba, ta ce. Ta ce zuwanta na karshe da ta je Fatakwal sayen jaririn, ‘yar uwartan ta rakota saboda a lokacin bata jin dadi.
Jaririn karshe da ta saya ta biya naira miliyan daya da dubu dari daya (N1.1m), a lokacin da ake tambayar ta, ta ce jaririn da take kokarin siya suna yin ciniki ne akan naira miliyan daya, inda ta ce tana so ita kuma ta sayar da shi ta samu ribar dubu dari.
An same ta da naira miliyan daya da dubu dari daya a cikin jaka, inda ta ce wanda zai sayi jaririn ne ya bata kudin a lokacin da ta baro Umuahia.
Da aka tambayeta wanda take shirin bawa kudin sai ta nuna wata mata a cikin kungiyar ta su mai suna Chi Chi. Da aka tambayi Chi Chi inda take kokarin samo jaririn sai ta nuna wata mata mai suna Aunty Ify. Ta ce Aunty Ify ta same ta inda ta bayyana mata cewa tana da jariri na sayarwa akan naira dubu 950, ita kuma sai ta dora ribar dubu hamsin ta sayarwa da Mrs Nwokocha akan naira miliyan daya. Ta ce idan Mrs Nwokocha ta bata kudin za ta bawa Aunty Ify kasonta, inda ita kuma Aunty Ify za ta kawo jaririn.
Da aka tambayi Aunty Ify inda ta samo jaririn da za ta sayar, ta ce ita ma bata sani ba. Ta ce ita ma wasu ne suka kira ta a waya cewa suna da jariri da za su sayar.
An tambayi Mrs Roseline Nwokocha abinda tayi da jaririn da ta sayar mako biyu da suka wuce, sai ta ce jaririn yana Aba tare da wasu ma’aurata. Da aka tambayeta sunayen ma’auratan ta kasa bayar da amsa.
Haka kuma an tambayeta mai take shirin yi da jaririn da ta zo za ta siya, sai ta ce wasu ma’aurata ne a Umuahia za su raini yaron. Haka suma ma’auratan na Umuahia ta ce ba ta san sunayensu ba.
Mace ta biyar a cikin kungiyar ita ce mahaifiyar jaririn da Mrs Nwokocha ta saya a wurinta mako biyu da suka wuce.
Ga dai bidiyon mutanen a lokacin da suke amsa laifinsu:
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Matar da ta kware wajen saye da sayar da jarirai ta shiga hannu yayin da take cinikin wani sabon jariri"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?