--
Mata ta shaƙe mijinta ya mutu yayin da suka samu sabani a gida

Mata ta shaƙe mijinta ya mutu yayin da suka samu sabani a gida



Rundunar 'Yan sanda a jihar Abia ta kama wata Mrs Rose Uwaga a kan zargin sheke mijinta mai shekara 83, Alhaji Isa Uwaga a Umuahia babban birnin jihar. Kakakin rundunar ta jihar, Geoffrey Ogbonnaya ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN,

 kama matar mai shekaru 73 a garin Umuahia a ranar Laraba. Ogbonnaya ya ce daya daga cikin yayan Uwaga, Ibeabuchi, na ya kai wa 'yan sanda rahoto a kan lamarin a ranar 2 ga watan Yuli. Ya ce an mika binciken zuwa sashin binciken manyan laifuka na 'yan sandan wato CID domin zurfafa bincike.

Ya kuma ce gawar mamacin tana dajin ajiye gawa na asibiti "inda ake sa ran gudanar da bincike a kan ta don sanin anihin abinda ya kashe mutumin." NAN ta gano cewar ma'auratan sun samu rashin jituwa har ta kai ga dambacewa a gidan su da ke Ohobo-Afara Umuahia. "Yayin fadar, mutumin ya dako adda domin ya firgita matar amma ta fi karfinsa ta murde hannunsa.

"Addar ta fadi daga hannunsa kuma matar da ke da girman jiki ta danne shi a kasa ta shake masa wuya har sai da ya mutu," a cewar wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa. Wani na kusa da iyalan da bayar da ba'asi ya ce akwai yiwuwar marigayin ya yanke jiki ya fadi ya mutu ne saboda gajiya bayan rikicin da suka yi da matarsa. Ya ce,

"Ba zai yiwu matar da shekarun ta suka kai 73 ta samu karfin sheke mutum har ya mutu ba." NAN ta ruwaito cewa iyalan mamacin sun taru za su birne shi bayan mutuwarsa bisa koyarwar addinin musulunci kafin Ibeabuchi ta sanar da 'yan sanda. Wacce ake zargin ta boye amma daga baya yan sanda sun kama ta.

A cewar wata majiyar 'yan sanda, Ibeabuchi ya bayyana a rahotonsa cewa iyayensa suna fada a lokacin da ya bar gidan. Majiyar ta kara da cewa, "Ya kara da cewa a lokacin da ya dawo gida, ya ga gawar mahaifinsa a zaune a kujera a gidan."

SOURCE: LEGIT.NG



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Mata ta shaƙe mijinta ya mutu yayin da suka samu sabani a gida "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?