Masu tireda sun yi zanga-zanga kan rushe musu rumfuna a bakin kasuwannin Kano
Monday, 20 July 2020
Comment
‘Yan tireda a kasuwar Sabongari sun nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira a matsayin zalunci yayin da Hukumar Kula da Sufuri ta Kano KAROTA ta rushe musu rumfuna da shaguna. Kwanaki uku da suka gabata ne Hukumar KAROTA ta yi rusau a wasu manyan kasuwanni na jihar Kano inda ta rushe fiye da shaguna 500 da ke wuraren da suka saba ka'ida a kan tituna.
A yau Litinin, 'yan kasuwa da wasu al'ummar gari sun yi zanga-zanga ta nuna bacin rai dangane da wannan lamari da wasunsu ke kira a matsayin toshe musu hanyar cin abinci. A wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta wallafa a shafinta na Twitter, ya hasko yadda wasu matasa ke zanga-zanga a bakin Kasuwar Singer daura da Kasuwar Sabon Gari.
Traders in Sabongari market have protested what they termed as illegal demolition of their shops by Kano Road Transport Agency.
Over 500 makeshift shops mounted along the main roads around the market were demolished about three days ago by KAROTA. pic.twitter.com/CRmkeSn3ZJ
— Daily Trust (@daily_trust) July 20, 2020Rahotanni sun bayyana cewa, an yi dan takaitaccen rikici tsakanin jami'an 'yan sanda da kuma wasu daga masu kasa kaya a gefen tituna a bakin kasuwar Sabon Gari.
Takaddamar ta auku ne a yayin da 'yan kasuwar ke gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin matakin da Gwamnatin Kano ta dauka na haramta kasa kaya a gefen titin kasuwar. Kwanaki uku da suka gabata ne gidan Rediyon Freedom ya ruwaito cewa, Hukumar KAROTA ta sanar da kammala duk wani shiri na kai simame wuraren da 'yan kasuwa ke kasa a kan tituna da wuraren da basu dace ba.
Shugaban Hukumar KAROTA, Alhaji Baffa Babba Dan Agundi, shi ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyarar gani da ido wuraren da aiki zai biyo takansu tun a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli. A yayin da yake zantawa da manema labarai,
Dan Agundi ya ce akwai fiye da shaguna dubu biyar da aka bari kara zube a gefen tituna da bakin kasuwanni a birnin Kano da kewaye. Daga cikin kasuwannin da shugaban KAROTA ya wassafa sun hadar da ta Sabuwar Tasha, Kwanar Ungogo, Unguwar Nassarawa, Yankin Masana'antu da kuma ta Sabon Gari.
Source: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Masu tireda sun yi zanga-zanga kan rushe musu rumfuna a bakin kasuwannin Kano "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?