
Maryam Sanda: Yadda wata mata ta yi hayar 'yan bindiga suka kashe mijinta
Saturday, 4 July 2020
Comment
Alkalin wata kotun majistare da ke zama a Fatakwal a ranar Alhamis ya bukaci a adana masa wata mata mai shekaru 40 a gidan gyaran hali.
Ana zargin Telma Bestman da laifin kashe mijinta mai suna Wagbara Bestman. An gano cewa, wacce ake zargin ta hada kai da wasu don su kashe mijinta da bindiga bayan sun samu rashin jituwa.
An gano cewa, wacce ake zargin tare da wadanda suka hada kai wurin kisan kan sun tarar da wanda suka kashe a gida mai lamba 15 titin Chiwota da ke Rumuolumeni a karamar hukumar Obio/Okpor ta jihar Ribas a ranar 13 ga watan Fabrairun 2020.
Wacce ake zargin kuma mahaifiyar yara hudun, tana fuskantar laifuka biyu da suka hada da kisan kai. Mai gabatar da kara, A. C Kennedy ya sanar da kotun cewa wannan laifin abun hukuntawa ne a karkashin sashi na 324 da 319 na dokokin laifukan jihar Ribas na 1999.
Alkali Ipalibo Iyiabo ya mayar da fayel na shari'ar zuwa ofishin gurfanarwa don neman shawara. Iyiabo kuma ya bukaci a adana wacce ake zargin a gidan gyaran hali tare da daga sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Augustan 2020.
A wani labari na daban, a ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2020, dan fashi da makami mai suna Adeniyi Ajayi, ya bayyana cewa matan aure da 'yan aiki yake wa fyade a kan idon mazansu don hakan ya zama ladabtarwa idan aka hana shi kudi yayin da yaje fashi da makami.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Adeniyi ya shiga hannun jami'an runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami ta jihar Legas. Sun kama shi a wani otel da ke yankin Ijora 7-up a jihar.
Adeniyi wanda ke fashi da makaminsa shi kadai, ya addabi jama'ar Sabo, Ijora Badia da sauransu. A lokacin da aka bayyana cewa an kama shi, mata takwas wadanda suka hada da ma'aikatan gwamnati da lauyoyi sun isa ofishin SARS don tabbatar da cewa ya yi musu fyade bayan fashi da makami da yayi.
'Yan mata biyu da ke aiki a wani kamfani a Sabo, sun ziyarci ofishin SARS inda suka bayyana yadda wanda ake zargin ya yi musu fyade a gaban abokan aikinsu maza, da rana tsaka a ranar 16 ga watan Yunin 2020.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Maryam Sanda: Yadda wata mata ta yi hayar 'yan bindiga suka kashe mijinta"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?