
Malaysia: An yanke wa Najib Razak hukunci kan badaƙalar $4.5bn na asusun 1MDB
Tuesday, 28 July 2020
Comment
![]() | ||
Tsohon firai ministan Malaysia Najib Razak yayin da ya isa wata kotu a Kuala Lumpur |
Wata kotu a Malaysia ta sami tsohon Firaiministan ƙasar Najib Razak da laifin amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba dangane da wata badaƙalar biliyoyin daloli da ake tuhumarsa da wawashewa daga asusun 1-M-D-B mallakin gwamnatin ƙasar.
Alkalin kotun ya kuma sami Mista Najib da hannu dumu-dumu kan wasu tuhume-tuhumen da suka jiɓanci cin hanci da rashawa da halatta kuɗin haram da zamba cikin aminci.
"Bayan yin nazari kan dukkan shaidun da aka gabatar a annan shari'a, ina ganin masu shigar da kara sun yi nasarar gabatar da hujjojinsu ba tare da shakku ba," in ji alkali Mohamad Nazlan Mohamad Ghazali na Babbar Kotun Kuala Lumpur.
Najib zai iya shafe shekara da shekaru daure a gidan yari - ko da yake ana sa ran zai ci gaba da walwala a waje har lokacin da za a kammala shari'a kan karar da zai daukaka.
Cikin tuhumar da ake masa, masu shigar da ƙara sun ce ya karkatar da miliyoyin daloli zuwa ga wani asusun ajiyarsa - kudin da ya rika facaka da su yana sayen kaya masu tsada da kuma kashe wasunsu ga jam'iyyarsa da a lokacin ta ke mulkin ƙasar.
Wannan shari'ar ita ce ta farko cikin jerin shari'un akalla guda uku da tsohon firaiministan ke fuskanta, wacce aka shafe wata 16 ana yinta.
Wadanne zarge-zarge aka yi masa?
Hukuncin da aka yanke ranar Talata ya shafi yadda aka wawashe dala biliyan 4 da rabi daga 1MDB - asusun da Mista Najib ya jagoranta da kansa - ta hanyar kafa wasu kamfanoni na bogi domin saye da mallakar kaya masu matukar tsada kamr gidajen da jiragen ruwa da attajirai kadai ke iya mallaka.
Sai dai ya daɗe yana musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa a kai, kuma har gabanin shari'ar magoya bayansa ƴan jam'iyyar United Malays National Organisation (UMNO), wadda aka kayar a watan Mayun 2018 bayan da badakkalar ta bayyana sun riƙa kare shi daga zargi.
Lauyoyin da ke kare Najib sun yi ikirarin cewa an fahimtar da shi cewa kudin da aka gano a asusunsa wata kyauta ce daga gidan Sarautar Saudiyya - ba kudi ba ne da ya karkatar da su.
Hukuncin da aka yanke zai iya sanya wa a daure shi tsawon shekara 15 zuwa 20 a kan kowanne guda daya. Kafin a yanke hukuncin, Najib ya ce zai daukaka kara idan aka same shi da laifi.
SOURCE: BBCHAUSA
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Malaysia: An yanke wa Najib Razak hukunci kan badaƙalar $4.5bn na asusun 1MDB"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?