--
Malamai, Sarakuna da ‘yan siyasa sun gabatar da taro kan rage sadaki da hana kayan lefe a Najeriya

Malamai, Sarakuna da ‘yan siyasa sun gabatar da taro kan rage sadaki da hana kayan lefe a Najeriya




A ranar Lahadi ne 12 ga watan Yuli, 2020, gamayyar manyan ‘yan siyasa, malaman addini da sarakunan gargajiya suka gudanar da wani gagarumin taro a cikin karamar hukumar Jega, dake jihar Kebb, don wayarwa da iyaye mata kai dangane da lamari da ya shafi aure.

Gamayyar sarakunan, malaman da ‘yan siyasar sun yi la’akari da halin da Najeriya ke ciki na tsananin talauci a wannan lokaci, hakan ya sanya suka bukaci hadin kan iyaye mata akan cire wasu abubuwa da basu da muhimmanci a lokacin aure, irinsu kayan lefe da kayan na gani ina so.


A lokacin taron dai an samu shawarwari da banbancin ra’ayi daga bangarorin, inda har ya zuwa wannan lokaci da muke rubuta wannan rahoto ba a bayyana ko sun samu matsaya ba, inda aka dage yin taron zuwa wani lokaci don a bawa ‘yan kwamiti isashen lokaci suyi nazari akan wannan lamari.

Bayan kammala wannan taro ‘yan jarida sun yi kokarin jin ta bakin wasu daga cikin matan akan wanna sabon al’amari, wata mai suna Hajiya Maryam ta nuna jin dadinta akan wannan sabon al’amari, inda ta ce koda naira dubu ashirin (N20,000) za a mayar da sadakin a shirye suke su tura ‘ya’yansu gidajen mazajensu, Hajiya Maryam ta ce a yanzu haka akwai yara mata guda hudu a gabanta wadanda duk sun isa aure.


Haka wata mai suna Aisha da take daya daga cikin ‘yan kwamitin taron, ta bayyana cewa sanya kudin aure mai yawa ga samari shine yasa ake samun koma baya wajen aure-aure, har wasu matan suka fada zinace-zinace, wannan daliline ya sanya ta nuna jin dadinta akan wannan taron.

Daga karshe Aisha tayi addu’ar Allah ya sanya wannan taro ya zama sanadiyyar kawo karshen lalacewar samari da ‘yan mata a jihar dama kasa baki daya.

SOURCE: PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Malamai, Sarakuna da ‘yan siyasa sun gabatar da taro kan rage sadaki da hana kayan lefe a Najeriya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?