Kaico: Likita ta mutu a Ribas kwana biyu da kammala hidimar kasa
Tuesday, 21 July 2020
Comment
Wata likita, Urenna Iroegbu, ta mutu bayan da wata motar haya wacce ta kasance a cikinta ta yi tukin ganganci, lamarin da ya haddasa hatsari a kan titin Onne, a birnin Fatakawal. Wannan lamari ya faru ne kwana biyu kacal bayan da Urenna ta kammala bautar kasa ta Hukumar NYSC.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Urenna ta kammala karatunta ne daga jami'ar jihar Imo inda ta shafe tsawon shekaru takwas wajen koyon aikin likitanci. A ranar Asabar ne Urenna ta hau wata motar kasuwa kirar Toyota Sienne daga jihar Akwa Ibom, inda tsautsayi ya sanya aka yi rashin sa'a ta mutu a kan hanya ba tare da riski gida ba.
An ruwaito cewa, tukin ganganci ya sanya direban motar da Urenna ta hau ya sabawa ka'idar tuki jim kadan bayan daukewar wani ruwan sama na mamako da ya sauka da misalin karfe 4.00 na Yamma.
Legit.ng ta fahimci cewa, wata babbar motar daukan kaya wadda ta ke kan hannunta na daidai, ta yi ciki da motar wadda Urenna ta kasance a ciki bayan direban ya hau hannun da ba nasa ba. Kwamandan hukumar kiyaye hadurra reshen jihar, Ayodele Kumapayi, ya mika lamarin a hannun hukumar 'yan sanda a reshen Onne.
Biyo bayan haka ne abokai da makusantan marigayiya Urenna, suka yi jimamin mutuwar Likitar a zaurukan sada zumunta. Wata aminiyar matashiyar da ta riga mu gidan gaskiya mai suna Martha Nduka, ta sanya hotunan abokiyarta a zauren sada zumunta na Facebook, inda ta bayyana damuwa a kan lamarin.
A wani rahoto na daban da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Hankula sun tashi a harabar Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Ogun, TRACE, a ranar Litinin bayan wani mutum, Fatai Salami ya kashe kansa a harabar hukumar.
A cewar rahotanni, Jami'an TRACE sun kama direban Salami ne ranar Alhamis 16 ga watan Yuli a Abeokuta saboda ya saba dokokin dakile annobar cutar coronavirus a jihar. An zargi cewa baya kiyaye dokar bayar da tazara a cikin motarsa kuma bai saka takunkumin rufe fuskarsa ba kamar yadda Linda Ikeji Blog ta ruwaito.
Source: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kaico: Likita ta mutu a Ribas kwana biyu da kammala hidimar kasa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?