Lauyan Magu zai nemi a saki tsohon Shugaban hukumar EFCC a yau Juma’a
Friday, 10 July 2020
Comment
A yau Juma’a, 10 ga watan Yuli, 2020, lauyan da ke kare Ibrahim Magu, ya ce zai gabatar da takarda gaban ‘yan sanda ya na neman a saki tsohon shugaban hukumar EFCC.
Barista Oluwatosin Ojaomo ya fadawa jaridar Punch cewa ya na shirin karbo belin Ibrahim Magu daga hannun jami’an tsaro. Oluwatosin Ojaomo ya bayyana cewa bai iya samun damar haduwa da Ibrahim Magu a ranar Alhamis ba,
duk da cewa ya dauki tsawon lokaci a ofishin ‘yan sanda ya na jiran tsammani. A jiya Lauyan ya bata lokaci har zuwa cikin dare a sashen binciken laifuffuka na CID da ke ofishin ‘yan sanda a unguwar Garki, babban birnin tarayya Abuja.
Lauyan ya shaidawa ‘yan jarida cewa: “Yanzu na ke barin FCID bayan na bata lokaci domin in sadu da Magu, amma ba su fito da shi daga fadar shugaban kasa ba.”
Ojaomo ya bayyana haka ne da kimanin karfe 8:30 na dare. A cewarsa, gobe (Yau kenan yanzu) zai nemi jami’an ‘yan sanda su saki Magu a kan beli. Ya ce: “Gobe zan rubuta takarda in gabatar a gaban ‘yan sanda domin a sake shi.”
”DIG ne kawai ya isa ya bada belinsa domin shi ya ke tsare da shi. Kuma ina kokarin in hadu da shi a game da lamarin.” Inji Lauyan. A game da halin da tsohon shugaban na EFCC ya ke ciki, Ojaomo ya ce a karshe Magu zai yi nasara, kuma babu dalilin a cigaba da tsare shi ba tare da iznin hukuma ba.
SOURCE: HUTUDOLE.COM
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Lauyan Magu zai nemi a saki tsohon Shugaban hukumar EFCC a yau Juma’a"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?