
Kudin Mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos ya karu da $13bn a ranar Litinin
Wednesday, 22 July 2020
Comment
Rahoton ya bayyana cewa arzikin Bezos ya karu ne a sakamakon kumburar da hannun jarin kamfaninsa ya yi da 7.9%, darajar da Amazon bai yi ba tun karshen 2018.
Masu nazarin tattalin arziki sun ce Amazon na kara samun karbuwa ne a sanadiyyar yadda jama’a su ke kara yi da kafafen hada-hada na zamani.
Da wannan makukun arziki, Bezos ya fi kamfanin Exxon, Mobil Corp., Nike Inc da McDonald’s Corp duk a dunkule kudi. Wannan kudi da Bezos ya samu a rana guda ya neman ribanya dukiyar Aliko Dangote biyu, wanda shi ne mai kudin kaf Nahiyar Afrika da kimanin Dala biliyan 7 a asusunsa. Idan ba za ku manta ba, a farkon shekarar nan Jeff Bezos ya rasa kusan Dala biliyan 10 a rana guda. Bayan nan Attajirin ya murmure, arzikinsa kuma ya fi na da.
SOURCE: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kudin Mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos ya karu da $13bn a ranar Litinin"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?