Kudin kiran waya zairagu da sako %40 cikin %100 anajeriya -Ncc
Monday, 13 July 2020
Comment
Za A Rage Kashi 40% Na Yawan Kudin Da Jama'a Suke Kashewa Wajen Yin Kira A Wayar Salula, Inji Ministan Sadarwa Sheikh Pantami
Ana sa ran cewa kudin da jama’a suke kashewa wajen yin kira a wayar salula zai ragu da kashi 40% bayan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa za a ga ragi a kudin waya bayan sun kwadaito da masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.
Dr. Isa Ibrahim Pantami ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shawo kan kalubalen da ake samu na kudin jawo igiyoyin RoW, da kuma tsare kayan aiki.
Sheikh Pantami ya yi wannan jawabi ne a wajen bude bikin koyon aiki da hukumar NITDA ta shirya wanda za ayi tsawon mako guda ana yi a birnin tarayya Abuja.
Ministan kasar ya shaidawa jama’a cewa cigaban da su ka kawo wajen kayan aikin sadarwa ya sa kamfanoni sun samu damar rage 40.18% na jama’a, daga 30% a shekarar bara.
Hukumar NITDA wanda ta ke karkashin ma’aikatar sadarwa ta shirya wannan taro ne ga ‘yan jarida domin samun kwarewa a harkar sadarwa ta zamani.
Mai girma ministan ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta na harin yadda farashin yin waya da hawa yanar gizo zai karye da 40% daga yanzu zuwa shekarar 2025.
A cewarsa, matakam da su ke dauka ya na cikin tsare-tsaren gwamnatin tarayya mai-ci na inganta harkar sadarwar zamani da kuma ragewa jama’a radadin rayuwa.
Har ila yau, ministan ya kara da cewa gwamnati za ta bada karfi wajen kwarewa a aiki a maimakon takardun shaida da digiri, wanda yin hakan zai kawo ayyukan yi a kasa.
Wannan horo da za a ba ‘yan jarida zai taimaka masu wajen inganta kwarewarsu a wurin aiki.
A karshe, ministan ya yi kira ga ‘yan jaridar da za a ba horo, su maida hankali wurin kawo rahoton gaskiya da adalci.
SOURCE: Shafin Rariya Na Facebook
Daga Comr Abba Sani Pantami
Daga Comr Abba Sani Pantami
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kudin kiran waya zairagu da sako %40 cikin %100 anajeriya -Ncc"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?