‘Ku bude asusun banki ko mu hana ku albashi’ - Hukumar Ilimi ta jihar sokoto
Tuesday, 21 July 2020
Comment
Shugaban Hukumar Ilimi a Matakin Farko a Jihar Sokoto, Shu’aibu Gwanda Gobir, ya gargadi malaman da ba su da asusun banki da cewa su gaugauta budewa ko su rasa albashinsu.
Ya ce gwamnatin jihar ba za ta amince da biyan albashin malamai ba a bisa tebur, kuma duk sakataren ilimin da aka kama yana yin hakan zai gane kurensa.
“Ku bude Asusun banki. Duk malamin da bai bude ba to ba za a biya shi albashin watan Yuli ba.” inji Gobir
Gobir, wanda ya nuna bacin ransa a wajen raba kayayyakin karatu ga kananan Hukumomi 23 na jihar, ya ce hukumar ta gaji da karbar korafin malaman na cewa ba su sami albashinsu ba.
Da ya ke nasa bayanin, Darakta mai kula da rarrabar kayayyakin hukumar, Kabiru Aliyu, ya ce an raba kayayyakin ne musamman ga wuraren karatu 1,420 da ba na boko ba.
Ya ce kayayyakin sun hada tufafin makaranta da jikkunan makaranta da allunan rubutu da dasta da ababen rubutu da kuma tabarmi.
Source: https://aminiya.dailytrust.com.ng/
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "‘Ku bude asusun banki ko mu hana ku albashi’ - Hukumar Ilimi ta jihar sokoto"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?