
Kokunsan Tsoffin gwamnoni hudu da Magu ya ɗaure alokacin yana shugaban hukumar EFCC?
Wednesday, 8 July 2020
Comment
Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'anati Ibrahim Magu ya tashi daga wanda yake farautar wasu zuwa wanda ake farautarsa.
A ranar Litinin 6 ga watan Yunin 2020 ne Magu ya bayyana gaban wani kwamiti a fadar shugaban kasa bisa zargin sa da aikata ba daidai ba.
Rahotanni sun ce Magu ya shafe daren ranar a hannun jami'an tsaro saboda kwamitin bai gama tuhumarsa ba.
Kafin yanzu dai Magu shi ne mai tuhumar mutane kan zargin almundahana tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi shugabancin EFCC a 2015.
Ya sha tsare manyan 'yan siyasar Najeriya har ma ya yi nasarar tura wasun su gidan yari bayan da kotu ta tabbatar da cewa lallai sun saci kudin kasa.
Ga dai jerin wasu manyan 'yan siyasa da Magu ya tura gidan yari a zamanin shugabancinsa:
Bala Ngilari
An yanke wa Bala Ngilari tsohon gwamnan jihar Adamawa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar bayan da EFCC ta zarge shi da rashin bin tsari wajen bayar da kwangila a lokacin da yake gwamna.
EFCC ta tuhumi tsohon gwamnan da wasu mutum biyu tare da kai su kotu kan cewa sun ba da kwangilar naira miliyan 167 ba bisa ka'ida ba.
Wata kotu a Yola ta samu gwamnan da laifi tare da daure shi tsawon shekara biyar, amma daga baya kotun daukaka kara ta jiha ta sauya hukuncin, inda ta ce tuhume-tuhuen da ake masa ba su da hujja.
Jolly Nyame
An yanke wa tsohon gwamnan Taraban hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari bayan kotu ta same shi da laifin almundahana da kudin gwamnati.
EFCC ta zargi gwamnan da satar kudin gwamnati a lokacin da yake gwamna tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.
Mai shari'a Adebukola Banjoko ya ce EFCC, karkashin shugabancin Magu, ta gabatar da hujjoji sosai kan yadda gwamnan ya wawure naira biliyan 1.64. Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli duk sun amince da hukuncin farkon, inda a yanzu gwamnan ke tsare a gidan yari.
Joshua Dariye
A shekarar 2007, EFCC ta tuhumi Joshua Dariye, tsohon gwamnan Filato da halatta kudin haram ta kuma ce ya sace naira biliyan 1.126 daga lalitar gwamnatin Filato.
EFCC ta ce ya sace kudin ne ta hanyar wani kamfani Ebenezer Reitner Ventures, wanda ba ma shi da rijista. Bayan shekara 10, Mai Shari'a Banjoko ya yanke masa hukuncin daurin shekara 16 a gidan yari.
Daga baya dai Dariye ya samu sassauci inda aka rage masa shekarun zuwa 10 bayan da Kotun Koli ta rage shekara hudu.
Orji Uzor Kalu
Orji Kalu yana sanata a lokacin da kotu ta tura shi gidan yari bayan da EFCC ta zarge shi da sace naira biliyan 7.65 tare da kwamishinansa na kudi a lokacin da yake gwamna.
A ranar 5 ga watan Disamban 2019 mai shari'a Mohammed Idris ya yanke wa tsohon gwamann hukuncin daurin shekara 12 a gidan yari amma daga baya Kotun Koli ya sake shi.
A yanzu Kalu ya kai karar EFCC kan zarginsa da ta yi da sata.
SOURCE: BBCHAUSA
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kokunsan Tsoffin gwamnoni hudu da Magu ya ɗaure alokacin yana shugaban hukumar EFCC?"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?