--
Kisan Gwaggon biri yajawa wani mutum daurin shekaru 11 agidan yari

Kisan Gwaggon biri yajawa wani mutum daurin shekaru 11 agidan yari


Wanda ya kashe wani goggon biri mai suna Rafiki, zai sha daurin shekaru 11 a kasar Uganda.

Felix Byamukama ya amsa laifin shiga cikin inda aka ajiye goggon birin sannan ya kuma kashe shi.

Da farko Byamukama ya ce goggon birin ne ya nemi hallaka shi sai shi kuma kare kansa ta hanyar kashe dabbar mai suna Rafiki.

Irin wadannan goggwan birran su 1,000 ne suka rage a duniya kamar yadda hukumar kula da namun dajin kasar Uganda ta bayyana.

Byamukama ya kuma amsa laifin kashe wasu dabobbin a cikin gidan namun dajin Uganda.
Bincike ya nuna cewa an kashe Rafiki ne da wani karfe mai kaifi da aka caka masa a ciki.

A ranar 1 ga watan Yuni ne goggon birin ya bace kuma sai washe gari sannan aka gano gawarsa.

Akwai kuma wasu mutane uku da ke jiran a yanke musu hukunci saboda batun kashe dabbar.

Shi wannan goggon biri ana kallonsa a matsayin shugaban iyalan dabbobi irinsa su 17.

Kuma su kuda sun saba da jama'a suna iya hudda da mutane ba tare da sun cutar da su ba.

Tsaunuka da goggon birran su ke na daga cikin wuraren bude ido a Uganda kuma kasar na samun kudin shiga tana wajen sosai.

Rafiki na da farin jini sosai a wajen gandun daji na Bwindi Impenetrable National Park.

Amma tun da annobar korona ta rikita lamura a duniya, sai aka samu karuwar mutanen da ke sando sukai hare-hare a wuraren da aka killace namun daji.

Tsaunukan da ke da goggon birrai na masun atukar kariya a kasashe Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda da kuma Uganda.

SOURCE: BBCHAUSA


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kisan Gwaggon biri yajawa wani mutum daurin shekaru 11 agidan yari"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?