
Kepa Arrizabalaga: kochin Chelsea Frank Lampard yana bukatar siyan sabon golan a wannan kakar
Tuesday, 28 July 2020
Comment
Kungiyoyi da yawa a kasar sifaniya suna da ra’ayin siyan Kepa Arrizabalaga,amma Chelsea suna so su mayar da makudan kudaden da suka biya wurin siyan golan nasu shekaru biyu da suka gabata euros miliyan 71. Lampard ya saka sunayen wasu gololin da yake ra’ayin siya wanda suka hada da Jan Oblak,Andre Onana da Nick Pope.
Athletico Madrid sun bayyana cewa Jan Oblak bana siyarwa bane, wanda hakan yake nufin idan har Chelsea suna da burin siyan shi to sai dai su biya makudan kudaden da kungiyar shi ta sa mai na farashin euros mikiyan 110.
Andre Onana zai fiwa Lamparda saukin siya saboda golan ya bayyana cewa yana so ya koma gasar Premier League kuma kunguyar Ajax zasu saurari duk kungiyar data bukace shi.Pope yana daya daga cikin kwararrun gololin Premier League na wannan kakar, yayin da golan ya buga wasanni 15 ba tare da an ci shi ba a kungiyar Burnley.
Ana sa ran Lampard zai fara yin amfani da Willy Ceballero a wasan karshe da zasu buga da Arsenal ranar sati na gasar FA Cup,kuma dama Willy ya maye gurbin Kepa Arrizabalaga a wasan da suka buga na karshe a gasar Premier League da Wolves.
SOURCE: HUTUDOLE.COM
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kepa Arrizabalaga: kochin Chelsea Frank Lampard yana bukatar siyan sabon golan a wannan kakar"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?