
Kashe Yan bindiga 46 a katsina katsinawa sun qaryata rundunar soji duba abinda sukace
Monday, 13 July 2020
Comment
Kungiyar BALDF ta mazauna karamar hukumar Batsari, ta yi watsi da jawabin da dakarun sojojin Najeriya su ka yi na cewa sun kashe wasu ‘yan bindiga 46 a harin da su ka kai. Sojojin Najeriya su na ikirarin sun kai harin gayya, inda su ka kashe ‘yan bindiga a Batsari.
“Mun godewa jami’an tsaro da su ke sadaukar da ransu domin ganin an samu zaman lafiya a karamar hukumar Batsari da jihar Katsina domin a cigaba da harkokin rayuwa.” Muslim ya kara da cewa: “Sai dai duk da haka, sai an kara kokari sosai, musamman a bangaren samun bayanai da kai samame ga miyagun da su ka sa rayuwa ta ke neman ta gagare mu.”
Shi ma hakimim garin Batsari, Alhaji Mohammed Muazu, a wata hira da ya yi ‘yan jarida ya koka da yadda ‘yan bindiga su ke jefa tsoro a zukatan al’ummarsa. Mai martaban ya ke cewa: “Mutane ba za su iya zuwa gonakinsu ba saboda gudun hare-hare. Har a cikin manyan garuruwa da kauyukan masarautar, mutane ba su iya barci da minshari.”
SOURCE: legit.ng
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kashe Yan bindiga 46 a katsina katsinawa sun qaryata rundunar soji duba abinda sukace"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?