--
Kano: An ƙwace kujerar ɗan majalisar APC an bawa PDP

Kano: An ƙwace kujerar ɗan majalisar APC an bawa PDP




Kotun zaben raba gardama na majalisar jihar Kano a ranar Juma'a ta soke zaben Magaji Zarewa na jam'iyyar APC mai wakiltar mazabar Rogo a jihar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Jibril Falgore, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya yi kara a kotu inda ya ke kallubalantar nasarar Zarewa a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 25 ga watan Janairu.

Sauran wadanda ya yi karar a kotun sun hada da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, da jam'iyyar APC kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito.

Alkalan uku karkashin jagorancin, Mai sharia A.M. Yakubu dukkansu sun amince da soke zaben Mr Zarewa a kan dalilin cewa bai yi murabus ba daga hukumar kula da shigo da magunguna da sauran ababen sha na jihar Kano kwanaki 30 kafin zabe ba,

kamar yadda yake a dokar tsayawa takara ta INEC. Kotun ta yanke hukuncin cewa Mr Falgore na jam'iyyar PDP shine hallastaccen zababben dan majalisa mai wakiltan mazabar Rogo.


Kotun ta umurci magatakardan majalisar jihar Kano ya rantsar da Jibril Falgore a matsayin zababben mamba mai wakiltar mazabar Rogo nan take ba tare da bata lokaci ba.

Lauyan wanda ya shigar da kara, Ibrahim Waru, a baya ya shaidawa kotu cewa Mr Zarewa ba bai cancanta ba ya sake takara a zaben rada gardama da za ayi a mazabar da Rogo.

Mr Waru ya roki kotun ta soke zaben Mr Zarwa inda ya bayyana cewa wanda aka yi karar bai yi murabus daga matsayinsa ba a matsayin shugaban Hukumar kula da shigo da magunguna da ababen sha kwanaki 30 kafin zabe.

SOURCE: LEGIT.NG

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kano: An ƙwace kujerar ɗan majalisar APC an bawa PDP "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?