Kana taka Allah na tashi: Amarya ta mutu ana tsaka da shagalin bikinta
Tuesday, 14 July 2020
Comment
‘Yan uwa da abokanan arziki sun shiga tashin hankali da rudani, bayan amaryar da suka taru domin taya ta murna ta fadi ta mutu ana tsaka da shagalin bikinta.
Amaryar mai suna Alexandra Erokhova, mai shekaru 25, ta mutu ana tsaka da yin walima a wani katon wurin biki dake kasar Rasha.
An ruwaito cewa amaryar ta ci wani abinci ne mai tsaki da ya sanyata ta fadi tace ga garinku nan.
Mutane cikin gaggawa suka garzaya domin taimakawa amaryar a yayin da ta fado daga kan kujerar da take zaune.
Sun kirawa motar asibiti zuwa wajen taron bikin da aka gabatar da shi a wani waje da ake kira da Tsaritsyno Palace dake cikin birnin Moscow, inda aka gabatar da bikin auren.
Bayan zuwan masu taimakon gaggawar sun kasa ceto rayuwar amaryar kamar dai yadda rahoto ya bayyana.
Likitoci sun bayyana dalilin da ya sanya ta mutuwar, inda suka ce sun yi imanin wata kwayar abince ce ta jawo hakan.
An gudanar da bikin auren ne a wani gidan sarauta da Mai Girma Catherine ta kafa, kuma dangin amaryar sun yi gargadi akan amaryar bata son irin wannan kwayar abinci.
Alexandra tana fama da wannan cuta ta rashin son wannan kwayar abinci tun tana yarinya, kuma an sanar da masu dafa abinci a wajen akan wannan rashin lafiya na ta, a cewar danginta.
Rahoton ya ruwaito cewa abincin da amaryar taci a ciki an sanya wannan kwayar abinci, duk kuwa da cewa ba a bayyana ainahin sunan wannan kwayar abinci ba.
Alexandra ta yi karatu a fannin kudi ne a kwalejin shugaban kasa ta Rasha, dake birnin Moscow.
‘Yan sanda dai suna gabatar da bincike game da wannan lamari a halin yanzu.
SOURCE: PRESSLIVES.COM
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kana taka Allah na tashi: Amarya ta mutu ana tsaka da shagalin bikinta"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?