--
Kalli vedion yanda ambaliyar ruwa ta kashe mata da 'ya'yanta huɗu a Abuja

Kalli vedion yanda ambaliyar ruwa ta kashe mata da 'ya'yanta huɗu a Abuja


Wata mata mai ciki tare da 'ya'yanta huɗu na cikin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a yankin Gwagwalada da ke Abuja, babban Birnin Tarayyar Najeriya.

Matar 'yar shekara 27 mai suna Habibat Hameed ta rasu tare da yaranta; Latifat da Rahamat da Abdulateef da kuma Rabiu, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Hotuna da bidiyo da aka wallafa a Twitter sun nuna yadda ruwa ya shafe gidaje da hanyoyin mota.




Jaridar ta ambato maƙwabcin marigayiyar mai suna Israel Musa yana bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:12 na daren Juma'a bayan ruwa ya shafe gidajen da ke kusa da wani kogi.

Ya ce matar na barci ne a ɗakinta tare da yaran nata a lokacin da ruwan ya cim musu.

Kazalika wasu mutum biyar ma sun mutu saboda ambaliyar ruwan da ruwan saman ya haifar a Suleja da ke Jihar Neja mai maƙwabtaka da Abuja tare da share wasu gidaje.

Mutum 10 ne suka rayukansu jumilla a Suleja.

Daily Trust ta ruwaito cewa an fara ruwan ne da misalin ƙarfe 4:00 na dare har zuwa 7:00 na safe a yankin.

SOURCE: bbchausa

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kalli vedion yanda ambaliyar ruwa ta kashe mata da 'ya'yanta huɗu a Abuja"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?