--
Kai dabba ne mai shan jinin al’umma – Fani-Kayode ya zagi gwamna Abdul’aziz Yari

Kai dabba ne mai shan jinin al’umma – Fani-Kayode ya zagi gwamna Abdul’aziz Yari


Tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, saboda kin bin ka’idojin cutar COVID-19 da aka sanya a filin jirgin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Da yake magana ta shafinsa na Twitter, FFK ya bayyana shi a matsayin, azzalumi, dabba, mai kashe mutane da kuma son kai.

Ya kara da cewa da a lokacin da yake ministan jiragen sama ne, ba zai sake bari Yari yayi tafiya a jirgin sama ba har abada.

Ya kuma yi alkawarin gaya masa hakan a duk lokacin da suka hadu ido da ido.

Ya ce: “Dama na sha cewa gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari dabba ne. Ba wai iya azzalumi ba ne mai hadama, ya shafe shekaru yana sha da kuma wanka da jinin mutanen shi ta hanyar taimakawa ‘yan bindiga.

“Yanzu har ya samu karfin guiwar cin mutuncin ma’aikatan filin jirgin sama na Aminu Kano, wadanda suka yi kokarin duba kayan shi ta hanyar sanya magani, saboda taurin kai yaki bin dokokin da gwamnatin tarayya ta sanya na COVID-19.

“Ya kamata hukumomi su sanya shi a keji kafin ya cutar da wasu mutanen. Ba shi da hankali kwata-kwata. Inda ace har yanzu nine akan kujerar ministan jiragen sama yayi wannan abu da ya gama hawa jirgi a rayuwar shi kenan.

“Wannan mutumin dan daba ne, kuma abin kunya ne ga mutanen jihar Zamfara, yankin Arewa dama Najeriya baki daya. Ba kowane yake tsoron shi ba, kuma lokaci yayi da gwamnatin tarayya da mutanen Najeriya za su dauki mataki a kanshi.








 SOURCE: PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kai dabba ne mai shan jinin al’umma – Fani-Kayode ya zagi gwamna Abdul’aziz Yari"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?