Hotunan tsohuwa mai shekaru 75 da tayi 'wuf' da mijin diyarta bayan rabuwarsu
Friday, 17 July 2020
Comment
Wata irin soyayya mai rikitarwa ta ratsa wasu iyalai a kasar Rasha. Tsohuwa mai shekaru 75 ce ake zargi da kwace saurayin diyarta bayan diyar ya ci amanarsa.
Mahaifiyar da diyar sun yi mugun fada mai cike da al'ajabi saboda saurayin. Shi kuwa babu kakkautawa ya koma wurin tsohuwar mai shekaru 75.
Matar mai suna Galina Zhukovskaya tana zama a St Petersburg a yankin yammacin Rasha na Leningrad Oblast. Ta aure tsohon mijin diyarta a 2010 bayan sun kulla alaka sakamakon cin amanarsa da diyarta take yi.
A lokacin da diyarta ta rabu da mijin nata, ta bai wa mijin matsuguni a gidanta wanda daga hakan soyayya ta kullu har suka yi aure.
A halin yanzu, tsohuwar tana kokawa da yadda diyarta mai suna Elena Podgornaya mai shekaru 56 take kokarin kwace mijinta mai suna Vyacheslav Zhukovsky mai shekaru 52.
Ta sanar da manema labarai cewa diyarta har yanzu bata samu masoyin da take fata ba tun bayan rabuwarta da tsohon masoyinta. Tsohuwar ta zargi diyarta da kishi, wanda yasa take son sake kwace tsohon mijinta daga hannun mahaifiyarta.
A yayin zantawa da wata mujalla ta Komsomolskaya Pravda, ta yi ikirarin cewa diyarta tana kokarin jan hankalin mijin mahaifiyar ta, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.
A wani labari na daban, Marina Balmasheva, 'yar asalin kasar Rasha ta aura dan kishiyarta mai shekaru 20 mai suna Vladimir Shavyrin, bayan rabuwarta da mahaifinsa.
Matar mai shekaru 35 ta wallafa bidiyon yadda suka yi auren kotu da dan nata. A halin yanzu, suna tsammanin haihuwa nan ba da dadewa ba, jaridar Daily Mail Online ta ruwaito.
A watan Mayu, Marina mai shekaru 35 ta bayyana labarin a yanar gizo, inda ta wallafa hotunanta tare da Vladimir a lokacin da yake da shekaru 7 a duniya.
A ranar aurensu, ta rubuta: "Mun isa wurin daurin auren. Ko gashina ban gyara ba. Zobban duk suna mota. Duk da farin cikin da muke ciki, akwai jin kunya kadan.
"Bayan daurin auren, mun saka kayan biki tare da jin dadinmu a wata liyafa da muka hada a wani gidan cin abinci. A halin yanzu ina da ciki kuma muna son komawa babban birni."
SOURCE: Legit.ng
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Hotunan tsohuwa mai shekaru 75 da tayi 'wuf' da mijin diyarta bayan rabuwarsu"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?