Hotuna: Saurayi yana nemawa mahaifiyar shi mai shekaru 60 mijin aure a shafin sadarwa
Tuesday, 14 July 2020
Comment
Mutane sun cika da mamaki bayan wani saurayi ya hau shafin sadarwa na Twitter ya sanar da cewa yana nemawa mahaifiyarshi mai shekaru 60 a duniya mijin aure, amma mai kudi.
Da yake wallafa hotunan mahaifiyarsa, saurayin wanda ya sanya sunanshi a Twitter kamar haka, @ajibade_adedapo, yayi bayanin cewa zai fi so ace mutumin da zai auri mahaifyarsan ya kasance bazawari wanda yake bai da mata, amma kuma mai kudi.
Ya ce: “Ina nemawa mahaifiyata mijin aure, shekarunta 60 a duniya. Idan kana da uba wanda ya rabu da matarsa ko kuma bai da mata, kuma yana da kudi, ku neme ni zamu iya zama ‘yan uwa.“
Wannan rubutu da ya wallafa ya jawo kace nace matuka a shafin na Twitter, inda wasu ma suke ganin cewa karya yake yi, wasu kuma suka ce babu yadda za ayi har ya sanya hoton mahaifiyarshi idan har ba da gaske yake yi ba.
SOURCE: PRESSLIVES.COM
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Hotuna: Saurayi yana nemawa mahaifiyar shi mai shekaru 60 mijin aure a shafin sadarwa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?