
Harin tawagar Zulum: Gwamnan Borno ya huce fushinsa a kan dakarun soji (Bidiyo)
Thursday, 30 July 2020
Comment
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Laraba ya nuna bacin ransa a kan yanayin aikin dakarun sojin da ke kokarin ganin bayan 'yan ta'addan Boko Haram a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar.
"Sama da shekara daya kuna nan, akwai soji 1,181 a nan. Idan ba za ku iya karbar Baga ba wacce take da nisan da bai kai kilomita biyar ba daga inda kuke, toh me kuke yi?
"Ina tunanin kawai mu hakura da Baga ko? Zan sanar da shugaban dakarun sojin da ya kwasheku ya kaiku inda za ku yi amfani. "Kun ce babu Boko Haram a nan, toh su waye suka kawo mana farmaki? Ina tantama idan aka ce babu Boko Haram a nan garin," gwamna Zulum ya tambaya.
Wasu wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai wa tawagar gwamnan hari a garin Baga a ranar Laraba. Ya jagoranci daruruwan jama'ar Kukawa, Cross da Baga zuwa tsohon garinsu bayan shekaru biyu da 'yan ta'addan suka kwace garin.
Tun farko, kwamandan Operation Lafiya Dole da ke Baga, Birgediya Janar Garba, ya tabbatar wa da Zulum da tawagarsa cewa babu 'yan ta'addan Boko Haram a garin. Gwamnan wanda ya je zagayawa, ya koma Maiduguri lafiya. Kafin ya bar Monguno zuwa Baga, Zulum ya gabatar da motocin sintiri 12 ga dakarun sojin Najeriya.
SOURCE: LEGIT.NG
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Harin tawagar Zulum: Gwamnan Borno ya huce fushinsa a kan dakarun soji (Bidiyo) "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?