--
First Bank na bawa mutanen da suke amfani da katin ATM na Verve kyautar man fetur

First Bank na bawa mutanen da suke amfani da katin ATM na Verve kyautar man fetur


Bankin Najeriya na FirstBank yana bayar da kyautar man fetur ga mutanen da suke amfani da katin ATM na bankin mai alamar Verve.

Bankin ya fara bayar da kyautar man fetur dinne ga masu katin Verve din tare da hadin guiwar kamfanin Oando, wanda aka fara a ranar 6 ga watan Yuli, kuma za a gama ranar 24 ga watan Yuli, 2020.

A yayin wannan garabasa, bankin ya ce, idan mutum ya sayi man fetur na N3,000 a gidan man Oando, za a bashi kyautar lita biyar ta mai a fadin jihar Legas a ranekun Litinin, Talata da Alhamis.

Gidajen man Oando da ake wannan garabasa sun hada da wadanda ke: Abijo (Lekki Stillwaters), Fola-Agoro, Maryland, Agege-Bypass, Lakowe, Lawanson, Ojodu-Berger, Alapere, Shiro Road (Fadeyi Ikorodu), Awolawo Road, kusa da ofishin hukumar kashe gobara, Marina da kuma na Tradefair.

Katin Verve dai kati ne na banki da ake amfani da shi wajen cire kudi a ATM, saye-saye a yanar gizo, sayen katin waya, biyan kudin wuta, ruwa, talabijin da sauransu.

SOURCE: PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "First Bank na bawa mutanen da suke amfani da katin ATM na Verve kyautar man fetur"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?