Fashewar karamin bam a harabar wani banki ya haddasa jikkatar mutane biyu
Thursday, 30 July 2020
Comment
Mutane biyu sun jikkata sakamakon fashewar karamin bam a harabar wani banki a jihar Oyo - Fashewar bam din ya faru ne sakamakon wani fashi da makami da akayi a bankin, wanda ya tilasta kwamishin 'yan sanda zuwa harabar bankin
Rundunar 'yan sandan ta ce hudu daga cikin 'yan fashin an cafke su kuma wasu fusatattu sun kona su Akalla mutane biyu ne ake hasashen sun jikkata bayan da wani bam ya fashe a yayin ziyarar da kwamishinan 'yan sanda na jihar Oyo,
Joe Enwonwu, ya kai wani bankin kasuwa. Ya kai ziyara a bankin ne a garin Okeho, jihar Oyo. Daga cikin wadanda suka jikkata bayan fashewar, akwai jami'in 'yan sanda da kuma wani farar hula. Rundunar 'yan sandan ta ce hudu daga cikin 'yan fashin an cafke su kuma wasu fusatattu sun kona su, yayin da rundunar ta samu nasarar cafke guda biyu.
Kakakin rundunar na jihar, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da fashewar bam din ga manema labarai a ranar Alhamis. A cewarsa, 'yan fashin a ranar Laraba sun bude kofar bankin ta hanyar harbi da bindiga kirar AK 47.
Bayan sun shiga suka shiga wani daki suka yi awon gaba da kudade masu yawa. Ya ce a lokacin da Mr Enwonwu ya ziyarci bankin a ranar Alhamis, an samu taruwar mutane cikin fusata, inda suka bukaci a basu 'yan fashin domin yanke masu hukunci.
Sai dai rundunar ba ta amince da bukatar mutanen ba, hakan ya sa jama'ar suka ki sauraron shugaban rundunar na matsawa nesa don samun damar yin bincike a wajen. Karamin bam din da ya fashe ya jikkata jami'in rundunar da kuma wani farar hula daga cikin jama'ar wajen.
Haka zalika, Mr Fadeyi ya ce fusatattun sunyi kokarin kaiwa 'yan sandan farmaki amma Mr Enwonmu ya ba jami'an umurnin barin wajen don gudun tayar da hargitsi.
SOURCE: LEGIT.NG
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Fashewar karamin bam a harabar wani banki ya haddasa jikkatar mutane biyu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?