--
Duniya ina zaki damu: Uwa ta yiwa jaririn da ta haifa yankan rago ta cire mishi makogwaro

Duniya ina zaki damu: Uwa ta yiwa jaririn da ta haifa yankan rago ta cire mishi makogwaro




An kama wata mata da zargin kashe jaririnta ta hanyar cire mishi makogwaro.

Jami’an tsaro sun kama matar a lokacin da suka iso wajen da lamarin ya faru a Preston Road, dake Wembley, yankin Arewa maso Yammacin London a ranar Laraba 22 ga watan Yuli.

Makwabtan ta wadanda hankalinsu ya tashi sakamakon lamarin, sun ce ta yanka makogwaron yaron ne kafin ta kwallawa wani mutumi da yake zaune a gidan kira.

Ilona Sidorova mai shekaru 45 da take zaune a kusa da matar ta bayyanawa The Sun cewa: “Na gano daga taga lokacin da ‘yan sanda suke yi mata tsawa. Na ganta a lokacin da ‘yan sandan suka tafi da ita.”

“Ni dai ban gani da idona ba, amma wani ya sanar dani cewa ta yankewa jaririnta wuya ne.”

Ta ce game da mutumin kuwa: ‘Saboda tsananin tsorata da yayi, sai da ‘yan sanda suka rike shi.”

Jami’an ‘yan sandan sun garzaya inda lamarin da ya faru da misalin karfe 9:51 na safiyar ranar Laraba, 22 ga watan Yuli bayan sun samu rahoto akan jaririn.

‘Yan sanda da jami’an lafiya na Landan sun isa gidan da lamarin ya faru, inda suka iske jariri wanda bai wuce shekara daya ba kwance babu rai.

Jami’an ‘yan sandan basu bayyana ainahin jaririn mace ce ko namiji ba, amma dai sun kama matar sun tafi da ita ofishinsu.


SOURCE: PRESSLIVES.COM

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duniya ina zaki damu: Uwa ta yiwa jaririn da ta haifa yankan rago ta cire mishi makogwaro"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?