--
Dumu-dumu aka kama dan siyasa yana yiwa yara kanana guda 2 fyade a cikin gidansa

Dumu-dumu aka kama dan siyasa yana yiwa yara kanana guda 2 fyade a cikin gidansa



An kama dan siyasa. Christopher Ogah, dumu-dumu yana lalata da wasu kananan yara guda biyu a cikin gidansa dake karamar hukumar Obi cikin jihar Nasarawa.

Wani shaida mai suna Oyikobi Ambassador, ya ce wanda ake zargin shugaban jam’iyyar APC ne na yankin Obi.

Ya ce yaran akwai mai shekara 12 da kuma mai shekara 13 da aka kama shi da su.

Haka wani shaida din wanda ya nemi a boye sunanshi, ya ce dan siyasar ya yaudari yaran ne a lokacin da suka shiga gidanshi su debi ruwa a rijiya.

Ya ce dama wannan ba wai shine karo na farko da aka taba kama mutumin da wannan laifi ba.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Mohammed Oyimoga Oyigye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace ya ceto rayuwar mutumin da tuni matasa sun sanya masa wuta, inda ya danka shi a hannun ‘yan sanda.

A nashi jawabin, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mr Bola Longe ya ce, “na bayar da umarnin a danka wannan lamari zuwa ga ofishin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) dake Lafia domin gabatar da bincike, inda daga nan za a kai mai laifin zuwa kotu.

“Yan sanda a karkashina suna gargadin masu fyade da su daina wannan al’adar ko kuma su hadu da fushin hukuma.

“Ina umartar rundunar ‘yan sanda da su kama kuma su hukunta duk wanda aka samu da irin wannan ta’asar ko wanene shi.”

SOURCE:PRESSLIVES.COM



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Dumu-dumu aka kama dan siyasa yana yiwa yara kanana guda 2 fyade a cikin gidansa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?