Duba Yanda Wani Soja yayi mankas da giya ya harbe mutum 13
Friday, 31 July 2020
Comment
Wani soja da ya sha barasa ya yi mankas, ya buɗe wa wasu fasinjoji wuta a kan hanya a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.
Rahotanni sun bayyana cewa sojan ya yi ajalin mutum 13 sa'annan kuma jama'a da dama suka samu raunuka.
Ɗaya daga cikin waɗanda sojan ya hallaka akwai wata yarinya 'yar shekara biyu.
Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Alhamis a kudancin lardin Kivu da ke gabashin ƙasar.
An daɗe ana zanga-zanga kan sojojin Congo da ke a garin Sange, inda aka toshe hanyoyi da dama.
SOURCE: bbchausa/
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Duba Yanda Wani Soja yayi mankas da giya ya harbe mutum 13"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?