
Duba Yanda Sojoji suka kona makaranta da gidaje a jihar Taraba
Saturday, 18 July 2020
Comment
An zargi sojojin Najeriya da kona gidajen mutane a garin Peva na karamar hukumar Takum a jihar Taraba.
Wasu mazauna garin sun shaidawa manema labarai na Punch cewa mutane na ta gudun tsira saboda wannan hari na bazata daga sojojin Najeriya.
Wani Mazaunin garin yace akwai wata makaranta me zaman kanta da wani mutum, Paul Gaza da sojojin suka lalata ta hanyar konawa da safiyar ranar, Asabar.
Sannan kuma sun kona gidajen wasu mutane. Shugaban kungiyar Kabikar Tiv reshen Takum, Peter Sule ya bayyana cewa sojojin sun taba yin irin wannan abu acan wani kauye
Yake idan masu laifi suke nema kamata yayi su kamasu amma su daina lalatawa mutane gine-ginen. Da yake magana kan lamarin, kwamandan rundunar yankin, Janar Adeyemi Yekini ya bayyana cewa haka kawai sojoji ba zasu je su rika kona gidaje babu dalili ba.
Source: hutudole.com
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Duba Yanda Sojoji suka kona makaranta da gidaje a jihar Taraba"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?