Duba yanda shugaban EFCC Ibrahim Magu yaso Arcewa yayinda Aka je kamoshi
Thursday, 9 July 2020
Comment
Rahoton yace an gayyaci Magu ta lalama sau da yawa amma yaki amsa gayyatar da aka masa. Dan haka ne aka tura a taho dashi ta karfin tsiya.
Wata majiya ta bayyana cewa da wanda aka aika su taho dashi suka sameshi a Ofis suka gaya mai ana son ya halarci zaman binciken da ake masa sai yace musu su bashi dama yayi sallah.
Ashe ba sallar yaje yi ba, kawai sai ya fice ta kofar baya, da niyyar arcewa, akwai wanda aka sa dama a bakin kofa, a nan ne suka tasa keyarsa zuwa Fadar shugaban kasa.
Vanguard ta ruwaito cewa majiyar ta kara da cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari yasan da zarge-zargen da akewa Magu amma yace kada a bincikeshi tukuna inda aka rika mai Daurin talala.
Ta kuma ce Magun yaki magana da masu binciken nashi a fadar shugaban kasa inda yace sai an kawo lauyansa tukuna, abinda yasa dole aka je aka kawo lauyan nasa.
Majiyar tace ana barin magu yaga Iyalinshi.
SOURCE: HUTUDOLE.COM
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Duba yanda shugaban EFCC Ibrahim Magu yaso Arcewa yayinda Aka je kamoshi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?