--
Duba Yanda Muƙamai da albashin ma'aikatan 'yan sanda yake a Najeriya

Duba Yanda Muƙamai da albashin ma'aikatan 'yan sanda yake a Najeriya



Rundunar 'yan sandan Najeriya Hoto daga Daily Trust Source: Twitter 


A ranar Asabar ne rundunar 'yan sandan Nigeria ta sanar da shirinta na neman daukar ma'aikata a rukunin shekarar 2020. Kakakin rundunar Frank Mba ya sanar da hakan yana mai cewa rundunar zata dauki mutanen da suka cancanta a mukamin kwanstabul, daga watan Yuli zuwa watan Agusta.


Frank Mba ya ce za a gudanar da matakan daukar aikin ne ta hanyar shigar da bayanai a shafin hukumar na yanar gizo. Ya bukaci masu sha'awar neman aikin da su ziyarci adireshin hukumar www.policerecruitment.gov.ng domin cike dukkanin bayanan da ake bukata. Mba ya yi nuni da cewa dole ne masu son neman aikin su cika duk wasu ka'idoji da aka zayyana a shafin hukumar na yanar gizo.

Ya ce za a gayyaci wadanda suka yi nasara zuwa tantancewa ta zahiri a manyan ofisoshin hukumar dake fadin jihohin kasar da suka hada babban ofishin hukumar na Abuja, daga ranar 24 ga watan zuwa 30 ga watan Agusta 2020.

Mai magana da yawun rundunar ya ce za a manna sunayen wadanda suka samu nasarar tantancewar a manyan jaridu na kasa a ranar 14 ga watan Satumba 2020 da kuma shafin hukumar na yanar gizo.

A wani rahoto da sashen Hausa na BBC ya ruwaito dangane da ababen da ya kamata a sani game da aikin ɗan sanda. Daga cikin abubuwar da jaridar ta fito da su fili sun haɗar da albashi da kuma makaman jami'an hukumar. Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadi, hukumar 'yan sanda ita ce babbar hukumar da ke tabbatar da tsaro da kiyaye doka a kasar.

Jagoran hukumar shi ne Babban Sufeton 'Yan Sanda na Najeriya. Su na da kwamishinoni a jihohi 36 da ke fadin kasar da kuma babban birnin tarayya. Kamar yadda mai magana da yawun hukumar a reshenta na jihar Ogun, Abimboa Opeyemi ya zayyana,

ana shiga aikin dan sanda domin kishin kasa ba don neman kudi ba. Ga albashin 'yan sandan Najeriya:

Kurtu: N46,000 zuwa N47,000

Kofu: N52,000-zuwa N53,000

Sajan: N62,000 zuwa N63,000

Mai anini 1: N78,000

Sufeto Anini 2: N123,000

ASP Mai Tauraro 1: N132,000 zuwa N134,000

ASP: N139,000 DSP: N142,000 zuwa N143,000.

Ga kuma jerin duk muƙaman 'yan sandan Najeriya Babban Sufeto Janar - Inspector General of Police (IGP)

Mataimakin Sufeto Janar na 'yan Sanda (DIG) Mataimakin Sufeto Janar na 'yan Sanda (AIG)

Kwamishinan 'Yan sanda (CP) Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda (DCP) Mataimakin

Kwamishinan 'Yan sanda (ACP) Babban Sufiritandan 'Yan Sanda (CSP) Sufritandan 'Yan Sanda (SP)

Mataimakin Sufiritandan 'Yan Sanda (DSP) Mataimakin Sufiritandan 'Yan Sanda (ASP) Sufetan 'Yan

Sanda (Inspector of Police)

Samanja Saje Kofur Las Kofur Kurtu

SOURCE: LEGIT.NG



TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓

Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/



FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/



TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice


LATSANAN DOMIN SAMUN

 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duba Yanda Muƙamai da albashin ma'aikatan 'yan sanda yake a Najeriya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?