--
Duba Yanda Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta

Duba Yanda Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta



Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta. Hoto daga The Nation Source: Twitter 

Marina Balmasheva, 'yar asalin kasar Rasha ta aura dan kishiyarta mai shekaru 20 mai suna Vladimir Shavyrin, bayan rabuwarta da mahaifinsa. Matar mai shekaru 35 ta wallafa bidiyon yadda suka yi auren kotu da dan nata.

 A halin yanzu, suna tsammanin haihuwa nan ba da dadewa ba, jaridar Daily Mail Online ta ruwaito. A watan Mayu, Marina mai shekaru 35 ta bayyana labarin a yanar gizo, inda ta wallafa hotunanta tare da Vladimir a lokacin da yake da shekaru 7 a duniya.
Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta. Hoto daga The Nation Source: Twitter 

A ranar aurensu, ta rubuta: "Mun isa wurin daurin auren. Ko gashina ban gyara ba. Zobban duk suna mota. Duk da farin cikin da muke ciki, akwai jin kunya kadan. "Bayan daurin auren, mun saka kayan biki tare da jin dadinmu a wata liyafa da muka hada a wani gidan cin abinci. A halin yanzu ina da ciki kuma muna son komawa babban birni."
Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta. Hoto daga The Nation Source: Twitter 

Matar 'yar asalin yammacin Krasnodar Krai, na zama da mijinta mai suna Alexey mai shekaru 45 kafin rabuwarsu. Sun yi zaman aure tun daga 2007 kafin su rabu sannan ta aure dan sa. Marina ta bayyana cewa basu magana da tsohon mijinta. "Ina tsammanin bai ji dadin abinda muka yi ba," tace.

SOURCE: LEGIT.NG

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duba Yanda Matar aure ta rabu da mijinta, ta aure dan mijinta "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?