--
Duba Yanda kamfanin TikTok ya goge bidiyo miliyan 49 da ke yaɗa batsa

Duba Yanda kamfanin TikTok ya goge bidiyo miliyan 49 da ke yaɗa batsa

TikTok ya goge bidiyo miliyan 49 da suka karya ƙai'idojinsa tsakanin watan Yuli zuwa Disamban 2019.

Kashi daya bisa hudu na wadanan bidiyon na kunshe da tsiraicin mutane da ayyukan batsa, a cewar sabon rahotan da manhajar ta fitar.

Manhajar yada bidiyo ta bankado yadda ta karbi bukatu 500 na neman bayanan mutane daga gwamnatoci da 'yan sanda, kuma ta amsa 480 cikin wadannan bukatu.

Amurka ta ce tana duba yiwuwar "haramta" shafin mallakin China.

A ranar Litinin, Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana cewa amfani da shafin TikTok tamkar "mika bayanan mutum ne a hannun gwamnatin China da Jam'iyyar Communist ke mulka".

Ya kara da cewa gwamnatin Amurka na duba yiwuwar ko za ta haramta amfani da shafin na China: "Da gaske muke a kan wannan batu. Muna duba batun sosai," a cewarsa, a tattaunawarsa da tashar Fox.

Gwamnatin India dai tuni ta haramta amfani da manhajar, kan dalilan da ta danganta da cin zarafi ta intanet.

TikTok mallakar wani kamfanin China ne, ByteDance. Sai dai ba a amfani da manhajar a China, amma ByteDance na amfani da makamanciyar wannan manhajar mai suna Douyin.

TikTok ya ce bai karbi wasu bukatu ba daga gwamnati ko 'yan sandan China kan bayanan mutane ba, haka zalika bai karbi wata bukata daga gwamnatin China na goge wani shafin mutum ba.

A ranar Alhamis, mujallar Wall Street ta wallafa rahoto da ke cewa kamfanin kasuwancin na duba yiwuwar bude sabuwar hedikwata a wajen birnin China.

TikTok ya shaida wa BBC a wata sanarwa cewa: "Lura da burinmu shi ne ci gaba. ByteDance na duba yiwuwar sauye-sauye kan ayyukansa da suka shafi TikTok.

''Burinmu shine kare muradai da bayanan masu amfani da shafinmu da kuma tsaro. Mun kikiri wannan mahanjar da niyyar fito da hazaka da kawo farin ciki a fuskar miliyoyin mabiyanmu a fadin duniya."

Tsarin Sirri
Mahukunta a Amurka na nazari kan ko TikTok ya mutunta yarjejeniyar 2019 kan kare bayanan sirrin 'yan kasa da shekara 13.

Manhajar ta ce ta takaitawa, da ba da tsaro bin dokokin da aka shimfida kan 'yan kasa da shekaru 13.

Ga bayanan rahoton TikTok:

Kashi 25.5% na bidiyon da ya goge na kunshe da batsa da tsiraici
Kashi 24.8% ya karya dokokin kare yara, kamar jefa yaro cikin muggan laifi ko halayye
Kashi 21.5% sun gudanar da ayyukan da suka saba shari'a
Kashi 3% an cire su saboda cin zarafi da tsangwama
Kasa da kashi 1% an goge su saboda kalaman nuna kiyayya.

RahotonTikTok ya bankado wadannan bayanai:
Bidiyo miliyan 49 da manhajar ta goge bai kai kashi daya bisa 100 na yawan bidiyon da aka wallafa a shafinsa ba tsakanin Yuli zuwa Disamban 2019
Kashi 98.2 cikin 100 na bidyon da aka goge na'urar da ke sa ido kan ayyukan manhajar ce ta gano su.

Sharhi, Daga James Clayton, Wakilin BBC kan fasaha da ke Arewacin Amurka
A shekarar 2017 aka kirkiri TikTok - kuma saboda bai jima ba har yanzu bai yi fice ba kamar Facebook, a misali.

Wannan rahoto ya dan yi bayani kan irin abubuwan da shafin ya kunsa.

Kwanan nan ana mayar da hankali kan shafukan da ke ba da kafa ga kiyayya da tsattsauran ra'ayi kamar Tiktok, sai dai ana sake jan hankali kan wallafa abubuwan batsa da wadanda suka shafi tsaro.

Sai gashi kusan rabin bidiyon daya goge ya fada a wannan rukunin.

Abin da bamu sani ba, shi ne yawan bidiyon kiyayya ko wanda ba su dace ba da watakil na'ura ko masu sa ido a shafin ba su kula da su ba.

SOURCE: BBCHAUSA


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duba Yanda kamfanin TikTok ya goge bidiyo miliyan 49 da ke yaɗa batsa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?