Duba Yanda Gwamnatin Najeriya Ta Kori Ma'aikatan Kamfanin Man Fetur Guda 850 Daga Aiki
Tuesday, 14 July 2020
Comment
Katafaren Kamfanin man Nijeriya na NNPC ya kori ma’aikatan sa 850 kuma akasarin su sun fito ne daga matatun man kasar da basa aiki yadda ya dace.
Sakataren kungiyar manyan ma’aikatan man kasar na PENGASSAN, Lumumba Okugbawa yace ma’aikatan da aka sallama sun kunshi kwararru da wadanda ba kwararru ba, tare da wadanda ke taimakawa wajen tafiyar da matatun man.
Kamfanin man NNPC bai yi bayani kan korar ma’aikatan ba, sai dai a makwannin da suka gabata, shugaban sa Mele Kyari ya bayyana damuwa kan asarar da kamfanin keyi wajen rashin ingantaccen aikin da matatun man kasar keyi, abinda ya sa Najeriya ta dogara da kasashen ketare domin samarwa al’ummar kasar tacaccen man fetur.
A watan Mayun da ya gabata, kamfanin NNPC yace yana da ma’aikata sama da 6,600 dake karbar albashi daga lalitar sa.
Nijeriya na daya daga cikin kasashen da suka dogara da albarkatun man fetur domin samun kudaden shigar da take amfani da su.
Source : Shafin Rarariya Na Facebook
Daga Comr Abba Sani Pantami
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Duba Yanda Gwamnatin Najeriya Ta Kori Ma'aikatan Kamfanin Man Fetur Guda 850 Daga Aiki"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?