--
Duba Yanda Aka kama wani magidanci da ke luwadi da kananan yara a Bauchi

Duba Yanda Aka kama wani magidanci da ke luwadi da kananan yara a Bauchi



Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta kama wani magidanci mai shekara 45, Nasiru Ibrahim da ake zargi da yin luwadi da dansa mai shekara biyar da wani yaro mai shekara takwas a garin Bauchi.


Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Ahmed Mohammed Wakili ne ya fitar da sanarwar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.


Sanawar da Wakili ya fitar ta ce, "A ranar 18/06/2020, wani Abdulkarim Jibrin mai shekara 45 a garin Zango na jihar Bauchi ya kai rahoto ofishin yan sanda da ke Tanshi kan cewa wani Nasiru Ibrahim ya tisa keyar dansa zuwa daki ya yi lalata da shi ta dubura a lokuta daban daban."


An kama wanda ake zargin kuma ya amsa cewa ya aikata laifin da ake zarginsa da aikatawar.


Ya ce wanda ake zargin ya kuma bayyana cewa ya aikata irin wannan lalatar da wani Yusuf Abdulkarim mai shekara 8 da wani Mujahid Abdulkarim mai shekara 7.

Sanarwar ta ce binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa wanda ake zargin yana dauke da kwayar cutar hepatitis B. Har wa yau, sanarwar ta kuma tabbatar da kama wani mai fyaden,


Rilwanu Adamu mai shekara 17 da ya yi wa wata yarinya mai shekara goma dabara suka tafi rafi a garin Dambam inda ya yi mata fyade. Shima wanda ake zargin ya amsa laifinsa a cewar sanarwar.

A wani labarin daban, Rundunar ƴan Sandan Jihar Adamawa ta kama wani magidanci mai shekaru 42 da ake zargi da lalata da ƴar cikinsa mai shekaru 17 har da lamarin ya kai ta samu juna biyu.


Kakakin rundunar ƴan Sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Alhamis a Yola. Nguroje ya ce kama magidanci da rundunar ta yi wani nasara ne da suke samu wurin yaƙi da fyade a jihar.


"Yan sanda na samun nasara a yakin da masu fyade da cin zarafin mata da yara a jihar. "Rundunar a ranar 1 ga watan Yuli ta kama wani mutum mai shekara 42, Matthew Joseph, mazaunin karamar hukumar Yola ta Kudu kan yin lalata da yarsa mai shekara 17.


"Wanda ake zargin ya fara lalata da yarsa ne bayan ya saki mahaifiyarta kimanin shekara guda kuma ya rika lalata da ita har sai da ta samu juna biyu. "Binciken da aka gudanar kawo yanzu ya nuna wacce abin ya faru da ita tana dauke da juna biyu na watanni uku kuma likitoci suna duba ta,"


in ji Nguroje. Yace rundunar yan sandan ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin ladabtar da duk wanda aka samu da laifi a lamarin.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Duba Yanda Aka kama wani magidanci da ke luwadi da kananan yara a Bauchi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?