
Duba Yadda Bam ya hallaka yara 6 kuma ya jikkata 5 a Malumfashi (Hotuna)
Saturday, 18 July 2020
Comment
Akalla yara biyar sun rasa rayukansu yayinda shida sunyi mumunan jikkata bayan Bam ya tashi da su a kauyen 'Yar mama dake karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina. Hukumar yan sandan jihar sun ce yara biyar suka mutu amma masu idanuwan shaida sun bayyana cewa yara 6 ne. Wannan abu ya faru ne yau Asabar, 18 ga watan Yuli, 2020.
Bisa jawabin da kakakin hukumar, Gambo Isha, ya ski, tashin Bam din ya auku ne cikin gonan wani Malam Hussaini Mai Kwai. Ya ce hukumar ta kaddamar da bincike cikin lamarin. Gambo Isah ya bayyana cewa yara guda 11 na yankan ciyawa ne don ciyar da dabbobi lokacin da abin ya auku. Yayinda biyar suka mutu kai tsaye lokacin, an garzaya da shida Asibitin garin Malumfashi domin jinya.
Source: Legit.ng
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Duba Yadda Bam ya hallaka yara 6 kuma ya jikkata 5 a Malumfashi (Hotuna) "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?