--
Duba Yadda aka kusa sake kama Magu ranar Alhamis

Duba Yadda aka kusa sake kama Magu ranar Alhamis


Saura kiris, da Magu ya sake komawa hannun yan sanda  Bayan kwashe kwanaki 9 a tsare, Magu ya nuna alamun rashin amincewa da dakatad da shi  Da wuri ya tsere daga gidan gwamnati dake Maitama zuwa na sa dake unguwar Karu Shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu, ya tsallake rijiya da baya ranar Alhamis kan cigaba da zamansa a gidan gwamnati.

Bayan ministan shari'a ya sanar da cewa shugaba Buhari ya dakatad da shi daga kujerarsa kuma an nada wani rikon kwarya, Magu ya cigaba da zama a gidan da gwamnati maimakon sabon shugaban. Bayan kwashe kwanaki 9 a tsare hannun jami'an FCID, an bada belin Magi da yammacin Laraba bisa umurnin kwamitin fadar shugaban kasa kan bincikensa karkashin Alkali Ayo Salami.

An tsare Magu ne a ofishin sashen binciken hukumar yan sanda dake unguwar Garki Abuja, misalin karfe 10 na safe ranar Litnin, 6 ga watan Yuli zuwa ranar Laraba, 15 ga Yuli. Daga sakeshi, Magu ya garzaya gidan da gwamnati ta tanadarwa shugaban EFCC a unguwar Maitama, kuma nan ya kwana.

Jaridar Tribune ta samu rahoton majiya cewa wannan abu da Magu yayi da kuma umurnin da ya baiwa jami'an tsaron da ke gadin gidan ya nuna cewa yana kokarin fito-na-fito da gwamnati; duk da cewa an dakatad da shi kuma an nada wani rikon kwarya. Da Magu ya samu labarin cewa ana kokarin sake damkeshi dalilin haka, sai ya tattara kayansa ya koma ainihin gidansa dake unguwar Karu da sassafiya Alhamis.

Ga jerin tuhume-tuhume 10 cikin 22 da ake yiwa Ibrahim Magu

1. Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato hannun barayin gwamnati

2. Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn

3. Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya

4. Rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya

5. Bata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda ahakan ya kai ga rikicin da ake a Kotu yanzu

6. Kin bin umurnin kotu na sakin asusun wani tsohon diraktan banki kimanin N7bn

7. Bata lokaci wajen daukan mataki kan jiragen ruwa biyu da hukumar Sojin ruwa ta kwace

8. Fifita wasu jami'an EFCC kan wasu wadanda akafi sani da 'Magu Boys'

9. Kai wasu Alkalai kara wajen shugabanninsu ba tare da sanar da Antoni Janar ba

SOURCE: LEGIT.NG

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Duba Yadda aka kusa sake kama Magu ranar Alhamis "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?