Duba Mutune 6 da zasu maimaita hidimar kasa a Kano - NYSC
Thursday, 16 July 2020
Comment
Hukumar NYSC a jihar Kano za ta tilastawa mutum shida su maimaita shekara daya ta bautar kasa a jihar - Hajiya Aisha Mohammad, shugabar hukumar NYSC ta jihar ce ta sanar da wannan labarin kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito
A cewarta laifinsu dai shi ne rashin tsayawa su kiyaye dokokin da hukumar ta shar'anta musu A ranar da wasu ke farin ciki na kammala bautar kasa ta NYSC, wasu ko murnarsu ta koma ciki a sakamakon wajabta musu maimaita shekara daya ta bautar da za su yi a jihar Kano. Hajiya Aisha Mohammad, shugabar hukumar NYSC ta jihar Kano,
Ita ce ta bada wannan sanarwa a yayin bikin yaye rukuni na biyu na masu hidimar kasar da suka kammala a bana. Aisha ta bayyana cewa, mutanen shida ne za su maimaita shekara guda ta bautar kasa, yayin da kuma hukumar ta tsawaita hidimar wasu mutum 16 sakamakon laifuka iri-iri da suka aikata.
aridar The Punch ta ruwaito cewa, an yi bikin gabatar da takardun shaidar kammala bautar kasar wanda aka gudanar a sakateriyar hukumar da ke kan titin Gwarzo a kanon Dabo. Kano State. Ta bayyana cewa, matasa 2,677 ne suka kammala bautar kasarsu salin alin a jihar Kano ba tare da samun wata tangarda ba.
Shugaban hukumar ta ce duk cikin masu bautar kasar babu wanda cutar korona ta harba har suka kammala hidimarsu ta tsawon shekara guda a jihar. Ta kara da cewa tuni hukumar ta yi tanadin duk wasu shirye-shiryen da suka wajaba don tabbatar da komawar masu bautar kasar zuwa jihohinsu na asali cikin aminci.
Ta gargade su a akan su tabbatar sun kasance sanye cikin kakin da hukumar ta basu na hidima yayin da zasu koma gidajen su
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, ya jagoranci wani taro na yanar gizo inda ya kaddamar da shirin fadar shugaban kasa na bunkasa hakar gwal (PAGMDI). Legit.ng ta ruwaito cewa, shirin PAGMDI zai samawa 'yan Nigeria akalla 250,000 ayyuka, yayin da gwamnatin tarayya za ta rika samun kudaden shiga $500m a kowacce shekara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Mista Femi Adesina ya fitar, ya ce shirin zai taimaka wajen kawo karshen hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da kuma baiwa Nigeria kwarin guiwar samun makoma mai kyau a nan gaba.
SOURCE: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Duba Mutune 6 da zasu maimaita hidimar kasa a Kano - NYSC "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?