--
Dan wasan Real Madrid Mariano Diaz ya kamu da cutar Covid-19

Dan wasan Real Madrid Mariano Diaz ya kamu da cutar Covid-19



Kungiyar Real Madrid ta yiwa yan wasan ta gwajin cutar korona yayin da suke shirin cigaba da gudanar da atisayi bayan ta basu hutun wasu kwanaki kadan, kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa Mariano Diaz ya kamu da annobar.

An yiwa yan wasan gwajin ne a gidajen su wanda haka ke nuna cewa Mariano bai kusanci wani abokin aikin shi ba. Dan wasan gaban yanzu zai killace kashi a gida tare da bin sharuddan cutar kamar yadda doka ta tanadar.

Real Madrid tayi jawabi akan sakamakon gwajin yayin data cewa, a jiya muka yiwa yan wasan mu na tawagar farko gwajin cutar Covid-19, kuma ma’aikatan lafiya sun tabbatar mana da cewa Mariano ya kamu da cutar. sun kara da cewa, dan wasan namu yana cikin koshin lafiya kuma zai killace kanshi a gida tare da bin dokokin cutar.

Sauran yan wasan Real Madrid sun cigaba da gudanar da atisayi a yau ranar talata, kuma Mariano ba zai samu damar buga wasan Madrid da Manchester City ba wanda za,a gudanar ranar 7 ga watan augusta.

SOURCE: HUTUDOLE.COM

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Dan wasan Real Madrid Mariano Diaz ya kamu da cutar Covid-19"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?