Dalibai na shirin fara zanga-zanga idan ba a bude makarantu ba a Najeriya
Friday, 17 July 2020
Comment
Daliban gaba da sakandare na Najeriya sun yi barazanar fara gabatar da zanga-zanga, idan har gwamnatin tarayya ba ta bayyana ranar da za a bude makarantu ba nan da mako biyu.
Daliban dai suna zaune a gida tun cikin watan Maris a lokacin da aka kulle makarantu sakamakon annobar coronavirus da ta addabi kasar.
Daliban karkashin kungiyoyin kwalejin ilimi dana jami’a, sun koka a wani taro da suka gabatar a yanar gizo, kan yadda gwamnatin tarayya ta nuna halin ko in kula dangane da bude makarantu a kasar.
Sun caccaki hukuncin da gwamnatin tarayyar ta yanke dangane da dakatar da rubuta jarrabawar WAEC a wannan shekarar, a cewar daliban za a iya rubuta jarrabawar ta WAEC kuma daliban su bi duka dokokin da aka gindaya.
“Zai yi matukar wahala ace za a iya kawar da annobar coronavirus cikin lokaci kankani, har yanzu babu wani sakamako mai kyau da aka samu dangane da hanyoyin da ake bi wajen yaki da wannan cutar.
“An kashe kudade masu tarin yawa wajen dakile cutar, amma har yanzu cibiyoyin yaki da cutar suna nan babu kayan aiki a fadin kasar,” suka ce.
Daliban sun bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da bawa malaman jami’a albashi da sauran manyan jami’o’i da suke goyon bayan cigaba da rufe makarantun, ba tare da bayar da wata kwakkwarar mafita ta kawo karshen annobar a Najeriya ba.
SOURCE: PRESSLIVES.COM
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Dalibai na shirin fara zanga-zanga idan ba a bude makarantu ba a Najeriya"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?