--
Da duminsa: An yi musayar wuta tsakanin magoya bayan APC da PDP a Edo

Da duminsa: An yi musayar wuta tsakanin magoya bayan APC da PDP a Edo



Wasu 'yan daba da ake zargin suna goyon bayan dan takarar jam'iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, sun gwabza da 'yan dabar da ke goyon bayan gwamna Godwin Obaseki, dan takarar jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Gungun 'yan dabar sun fafata a daura da fadar sarkin Benin, Oba Ewuare II, a ranar Asabar. Rahotanni sun bayyana cewa an yi musayar wuta yayin fafatwar 'yan dabar,

lamarin da ya haifar da rauna jama'a tare da lalata ababen hawa. Rikicin ya barke ne lokacin da gwamna Obaseki tare da sauran gwamnonin jam'iyyar PDP suka ziyarci fadar sarkin gabanin kaddamar da yakin neman zaben Obaseki a matsayin gwamnan jihar Edo a karo na biyu.

Source: Legit.ng.........

TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Da duminsa: An yi musayar wuta tsakanin magoya bayan APC da PDP a Edo "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?