
Da duminsa: Tsohon Kakakin Majalisa, Yakubu Dogara ya dawo APC
Friday, 24 July 2020
Comment
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Yakubu Dogara ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP ya koma APC. Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni ne ya tabbatar da hakan bayan ganawar da suka yi da Shugaba Buhari a yau Juma'a a Abuja.
Da aka tambaye shi ko Dogara ya koma APC, Shugaban kwamitin rikon na APC ya sama da cewa, "Eh, ya dawo."
An tambayi Buni ko dawowar Dogara APC na da alaƙa da zaɓen 2023, ya ce, "Eh, ba ma shirin zaɓen 2023 ba, muna saita jam'iyyar ne ta yadda ko bayan mu za ta cigaba da bunƙasa. "Ba batun yanzu kawai ake ba ko wani ƙanƙanin lokaci, ba maganan zaɓe bane ko yaƙin neman zabe, magana ce ta gina jam'iyya.
hakan zai sa jam'iyya ta ƙarfafa da kuma gina ta. Idan babu adalci, hakan ba zai yi su ba kuma muna da tabbacin zamu yi wa kowa adalci." Buni ya ce ya ziyarci shugaban kasa ne kan batun ƙoƙarin da su ke yi na gina jam'iyya kuma "ya sanar da shi cigaban da ake samu." Da ya ke tsokaci kan yadda shugaban kasa ya karbi labarin, ya ce, "Ya yi maraba da shi. Ya yi murna da abinda ya faru. Muna gina jam'iyya kuma hakan na cikin matakan da muke ɗauka na gina jam'iyyar."
SOURCE: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Da duminsa: Tsohon Kakakin Majalisa, Yakubu Dogara ya dawo APC "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?