
Da duminsa: Gwamnatin Jigawa ta soke bukukuwan babbar Sallah
Wednesday, 22 July 2020
Comment
Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya soke bukukuwan babbar Sallar Lahya a jihar da kuma dakatar da sarakuna biyar masu daraja na jihar daga jagorantar duk wani hawan Sallah ko hawan daushe a babbar Sallar wannan shekarar.
A cewarsa, "Manyan motoci 110 cikin 150 makare da kayan abinci sun iso cikin jihar kuma an turasu zuwa ga al'umomin da zasu ci gajiyar tallafin."
Ya jaddada cewa za ayi rabon kayan abincin ne a gundumomi 287 da ke a kananan hukumomi 27 da ke jihar. "Zamu tabbata kowa ya samu wannan tallafi domin za abi tsari mai kyau." Ya ce a wannan lokacin, "har yanzu mutum daya ne kawai ya rage a cibiyar killace masu dauke da cutar. An rufe cibiyon Fanisau da Birninkudu, amma suna a tsaftace don jiran ko ta kwana.
sabbin mutum 562 sun sake kamuwa da korona a Najeriya. Ga bayani daki-daki, jiha bayan jiha. FCT-102
Lagos-100
Plateau-52
Kwara-50
Abia-47
Kaduna-35
Benue-34
Oyo-26
Ebonyi-24
Kano-16
Niger-15
Anambra-14
Gombe-12
Edo-11
Rivers-6
Nasarawa-5
Delta-5
Borno-3
Enugu- 2
Bauchi-2
Kebbi- 1
Kamar yadda hukumar NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter, a yanzu jimillar mutane 37,225 ne ke dauke da cutar wadanda kuma suke kwance a gadon asibiti. Haka zalika, hukumar ta sanar da cewa, akwai jimillar mutane 15,333 da aka sallama daga asibiti bayan samun tabbacin warkewa daga cutar. A hannu daya kuma jimillar mutane 801 ne suka mutu sakamakon wannan cutar.
SOURCE: LEGIT.NG
TALLA: Sayi datar kowane network kamar: MTN, AIRTEL, GLO 9MOBILE mai inganci da rahusa latsa nan↓↓↓
Data Bundle Promo By BZ GLOBAL SERVICES
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Da duminsa: Gwamnatin Jigawa ta soke bukukuwan babbar Sallah "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?